Siyasar Najeriya
Jam'iyyar NNPP mai kayan alatu ta yi zargin cewa wasu da ake ea laƙabi da yan bindigan da ba a sani ba suna barazanar kai hari babban sakateriyar jam'iyyar ta ƙasa.
Fasto Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewa 'yan Najeriya na damunsa don ya tsaya neman takarar shugaban kasa inda su ka ce har kudin fom za su biya.
Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi karin haske kan dambarwan siyasar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsakaninsa da Gwamna Fubara.
Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Ondo sun bayyana cewa bai kamata a zuba ido a bar tattalin arzikim jihar na ja baya ba saboda rashin kataɓus ɗin gwamna.
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, kan butulcin da ya yi masa bayan ya hau kan mulkin jihar Rivers.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa mutum biyu a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta hukumar kwanstam ta kasa na tsawon shekara huɗu.
An samu tashin hankali a Kano, yayin da magoya bayan jam'iyyar NNPP suka yi gangamin salloli da addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda na kar su yi hakan.
A ranar Jumu'a 24 ga watan Nuwamba, 2023, kotun ɗaukaka kara mai zama a Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC a Ebonyi.
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta yi fatali da ƙarar Isah Ashiru Kudan da jam'iyyar PDP, waɗanda suka ɗaukaka ƙara suna kalubalantar nasarar Malam Uba Sani.
Siyasar Najeriya
Samu kari