Hannatu Musawa: Ministan Al'adu Na Tinubu Ta Magana Kan Matsayinta Na NYSC; Karin Bayani

Hannatu Musawa: Ministan Al'adu Na Tinubu Ta Magana Kan Matsayinta Na NYSC; Karin Bayani

  • Hannatu Musawa, Ministan Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira, ta nesanta kanta daga maganan da aka rahoto ta yi game da rudanin kasancewarta yar NYSC
  • Kungiyar Marubuta Masu Kare Hakkin Biladama, HURIWA, ne ta janyo hankali game da kasancewar ministan yar yi wa kasa hidima
  • Amma, wani sanarwa da Musawa ta nesanta kanta da shi na ikirarin cewa babu wani doka da ya hana mai yi wa kasa hidima rike mukamin siyasa

FCT, Abuja - Hannatu Musawa, Ministan Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira ta nesanta kanta daga wani sanarwar da aka rahoto ta fitar game da cece-kuce da ake game da kasancewarta yar NYSC.

Wani rahoto da wasu kafafen watsa labarai suka fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa ministan a karshe ta magantu kan kasancewarta mai yi wa kasa hidima.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abin Da Shugaba Tinubu Ya Fadawa Ministoci A Taronsa Na Farko Da Su, Bayanai Sun Fito

Hannatu Musawa: Babu doka da ta hana dan NYSC zama minista
Hannatu Musawa ta ce babu doka da ta ce yan NYSC ba zai iya zama minista ba. Hoto: Photo credit: Barrister Hannatu Musawa
Asali: Facebook

Kungiyar Marubuta Masu Kare Hakkin Biladama, HURIWA, ne ta janyo hankali da cewa daya cikin ministocin Tinubu yi wa kasa hidima ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hannatu Musawa: Kakakin NYSC ya tabbatar wai cewa ita yar yi wa kasa hidima ne

A baya, Eddy Megwa, Diraktan Sashin Watsa Labarai na NYSC, ya ce rike minista da Musawa ke yi yayin da ta ke yi wa kasa hidima ya saba dokar NYSC.

Da ya ke magana, Megwa ya yi bayani cewa tanadin dokar NYSC ya ce dan yi wa kasa hidima ba zai iya karbar aikin gwamnati ba sai shekara guda bayan gama yakin.

NYSC: Babu dokar da na karya, an rahoto wai Musawa ta yi martani

A cikin wani sanarwa a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, an ce ministan ta yi bayanin dalilin da yasa ta jinkirta yi wa kasa hidiman har zuwa 2023.

Kara karanta wannan

NYSC: Hannatu Musawa Ta Sake Sabon Martani Game Da Bautar Kasa, Ta Gargadi Mutane

An kuma rahoto ta ce Akwa Ibom aka tura ta madadin Ebonyi, da Kakakin NYSC ya ce.

Ga wani sashi na sanarwar:

"Ina son in bayyana karara akasin bayanai na kuskure da wasu kafafen watsa labarai da dandalin sada zumunta suka yi, babu saba dokar Tarayyar Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a nadin da aka yi min na minista a matsayina na mai yi wa kasa hidima.
"Ya zama dole a sani cewa babu wani doka ko sashi na kundin tsarin kasa da dokar NYSC da ya ce Shugaban Kasa ko wani mai ikon nadi a doka ba zai iya nada dan yi wa kasa hidima mukami ba. Kazalika, babu wani sashi na dokar NYSC da ya ce dole mai yi wa kasa hidima zai ya kammala sannan za a iya masa nadin siyasa. Babu wata hujja ta doka da ya hana hakan. Babu wata doka ta Najeriya da na karya."

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa: Shin Masu Yi Wa Kasa Hidima Na Iya Zama Minista? Falana, Sauran Lauyoyi Sunyi Martani

NYSC: Musawa ta nesanta kanta daga sanarwar da ya bazu

A wani sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu a daren ranar Lahadi, Musawa ta ce sanarwar na baya ba daga bakinta ya fito ba, don haka, ta nesanta kanta daga abin da ya kunsa.

Suleiman Haruna, mataimakin direkta a Ma'aikatar Sadarwa da Wayar da Kan Yan Kasa ne ya fitar da sanarwar ta baya-baya.

Sanarwar ta ce:

"Hankalin Barrista Hannatu Musa Musawa, Ministan Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira ya kai kan wani sanarwa da ake yada wa:
"JAWABI NA KAN MATSAYIN NA NA MAI YI WA KASA HIDIMA". An danganta wannan sanarwar da ita bisa kuskure dangane da batun NYSC.
"Mai girma Minista na yin karin haske cewa ba ta fitar da wani sanarwa a hukumance ba dangane da batun da aka ambata kuma tana bukatar al'umma su yi taka tsan-tsan da batun wanda ba a tantance shi ba.

Kara karanta wannan

Ana Mulkin 'Yan Koyo: Shehu Sani Ya Jero Wadanda Ya Kamata Tinubu Ya Nada Ministoci

"Ina makukar godiya da bisa goyon baya, da fahimta da yan Najeriya ke nuna min a halin yanzu. Don karin haske, ina son bayyana cewa ban fitar da wani sanarwa kan batun ba."

Shin yan NYSC na iya zama minista? Lauyoyi sun yi martani

A bangare guda, manyan lauyoyi sun magantu kan abin da kundin tsarin mulki ya ce kan nadin Musawa a matsayin ministan fasaha, al'ada da tattalin arzikin fikira da Shugaba Tinubu ya yi.

Yayin da wasu lauyoyi suka ce kundin tsarin mulki ya amince da nadinta, wasu ra'ayinsu ya banbanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel