Abba Vs Gawuna: Jam'iyyar APC Ta Roki Magoya Baya Su Dauki Azumi

Abba Vs Gawuna: Jam'iyyar APC Ta Roki Magoya Baya Su Dauki Azumi

  • Siyasa ta ƙara zafi tsakanin jam'iyyar APC da NNPP mai mulkin Kano yayin da ake dakon hukuncin Kotu kan zaɓen gwamna
  • Jam'iyyar APC ta buƙaci 'ya'yanta su tashi da azumi kana su dage da rokon Allah ya ba su nasara a Kotun zaɓe
  • Sakataren APC na jihar ya ce wannan umarni ba bu tilas amma da yawan mambobi sun ɗauki azumin yau Litinin

Kano state - Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta umarci ɗaukacin mambobinta su ɗauki Azumi kana su ƙara matsa ƙaimi wajen roƙon Allah ya sa su samu nasara a Ƙotun zaɓe.

Sakataren APC na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa tuni 'ya'yan jam'iyyar na haƙiƙa suka fara bin wannan umarni na yin azumi da Addu'a.

Jam'iyyar APC reshen Kano.
Abba Vs Gawuna: Jam'iyyar APC Ta Roki Magoya Baya Su Dauki Azumi Hoto: OfficialAPCNg
Asali: UGC

Ya ce bayan APC ta bada wannan umarni, mafi akasarin mambobin jam'iyyar na jihar Kano sun tashi da Azumi yayin da suka ci gaba da addu'o'i a matakin gunduma da ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban Jam'iyya Ya Faɗi Wanda Yake da Tabbacin Zai Samu Nasara a Kotu

Wannan ci gaban na zuwa ne awanni 48 bayan jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta shirya babban taron addu'a wanda ya gudana ranar Asabar da ta shige.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NNPP ta gudanar da addu'o'in ne domin rokon Allah ya ba ta nasara a hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna zata yanke da kuma zaman lafiya a Kano.

Meyasa APC ta roki magoya bayanta su yi Azumi

A kalamansa, sakataren APC na jihar Kano ya ce:

"Kamar yadda kuka sani, mu ’yan dimokradiyya ne kuma ba mu yarda da ire-iren abubuwannan da suka yi kama da kungiyar asiri ba."
"Duba da yanayin matsin tattalin arzikin da ake ciki, mun ba da shawarin, babu tilas, cewa duk wanda zai iya yin azumi to ya yi, kuma da yawa sun ɗauka yau (Litinin)."

Ya kara da cewa an karkasa zaman taron addu’o’in a matakin unguwanni da kananan hukumomi domin a kaucewa duk wani yanayi da bai dace ba.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Siyasa ta yi zafi a Ƙano

Siyasar Kano ta kara daukar zafi tun lokacin da alkalin kotun zaɓe, Flora Azinge ya yi zargin cewa wasu lauyoyin na kokarin ba su cin hanci a madadin waɗanda su ke karewa.

Wannan batu dai ya tada ƙura a siyasar jihar Kano har ta kai ga manyan jam'iyyu masu hamayya da juna, APC da NNPP sun fara zargin juna da musayar yawu.

Ya Kamata Yan Najeriya Su Shiga Rudani Kamar Ni, Atiku Abubakar

A wani rahoton kuma Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake yin kalaman shaguɓe kan takardun karatun shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce a tunaninsa kowane ɗan Najeriya mai hankali kansa ya kulle kan takardun karatun Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel