'Yan Daba Sun Kai Hari Babbar Sakatariyar Jam'iyyar LP a Jihar Imo

'Yan Daba Sun Kai Hari Babbar Sakatariyar Jam'iyyar LP a Jihar Imo

  • Wasu 'yan daba sun kai farmaki sakatariyar jam'iyyar Labour Party da ke Owerri, babban birnin jihar Imo
  • Bayanai sun nuna cewa 'yan daban siyasan sun ruguza sakatariyar, sun sauke allunan tallan Peter Obi
  • Shugaban LP na jihar ya aike da sako ga IGP na ƙasa kan abinda ke faruwa, ya roƙi a kai musu ɗauki kan cin mutuncin da ake musu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Imo state - Wasu 'yan daba da ake zargin na siyasa ne sun kai farmaki Sakateriyar jam'iyyar Labour Party (LP) ta jihar Imo da ke Kudu maso Gabas.

Jaridar Tribune ta tattaro cewa 'yan daban sun rushe ginin Sakatariyar LP wacce ke kan titin Wethedral kusa da tsohuwar kasuwar katako a Owerri, babban birnin jihar Imo yayin harin.

Tutar jam'iyyar Labour Party.
'Yan Daba Sun Kai Hari Babbar Sakatariyar Jam'iyyar LP a Jihar Imo Hoto: LP
Asali: UGC

An tattaro cewa maharan sun rushe ginin wurin da sanyin safiyar ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023 a kan idon dakarun 'yan sanda, lamarin da ya ja hankalin mutane.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Tuni mazauna jihar Imo suka yi Allah wadai da wannan ɗanyen aikin wanda su ke zargin akwai hannun wasu manyan mutane domin naƙasa 'yan adawa gabanin zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

LP ta bukaci IGP ya kawo mata ɗauki

Shugaban LP na jihar Imo, Barista Calistus Ihejiagwa, ya aike da saƙo ga hedkwatar jam'iyyar ta ƙasa da kuma sufeta janar na yan sanda, inda ya roƙi a kawo musu ɗauki.

A rahoton Vanguard, ya ce:

"Da sanyin safiyar yau (jiya) Litinin 28 ga watan Agusta, ‘yan sanda da ‘yan baranda suka sake kai hari sakatariyar jam’iyyar LP ta jihar Imo bisa umarnin gwamnatin jiha."

Tun a baya, Ihejiagwa ya roƙi yan Najeriya da su agaza wa jam'iyyar ta tsira daga sharrin harin 'yan daba sama da 100 tare da haɗin guiwar jami'an 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Ɓarnar da 'yan daban suka yi wa LP

A cewarsa, baya ga lalata Sakatariyar jam’iyyar, ‘yan ta’addan sun kuma cire tutar jam’iyyar, allunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar watau Peter Obi da na ɗan takarar gwamna, Sanata Athan Achonu.

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa bayan haka sun lakaɗa wa shugabanni da ma'aikatan LP dukan tsiya kana suka yi awon gaɓa da wayoyinsu.

Ya ce: “Lokacin da muka tunkare su, sai suka ce suna karkashin umarnin gwamnatin jihar ne na kawar da allunan tallar Peter Obi da Sanata Athan amma musamman na Obi."

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Imo, ASP Henry Okoye, ya nuna ba shi da masaniya kan faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin gudanar da bincike.

Gwamnatin Adamawa Ta Siyo Motocin Sama da Biliyan Don Tallafa Wa Talakawa

A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Adamawa ta lale naira biliyan 1.06 ta siyo motocin Bas guda 10 domin agaza wa talakawa a fannin sufuri.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Auwal Tukur, ya ce nan ba da jimawa ba motocin zasu hau titi su ci gaba da aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel