Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Kano Ya karyata Labarin Dakatar Da Kwankwaso

Shugaban Jam'iyyar NNPP Na Kano Ya karyata Labarin Dakatar Da Kwankwaso

  • Shugaban jam'iyyaar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihar Kano ya ƙaryata labaran da ke cewa an dakatar da.Ƙwankwaso daga jam'iyyar
  • Hashimu Dunguruwa ya bayyana cewa a taron NEC na jam'iyyar sun ƙada.ƙuri'ar amincewa da Ƙwankwaso
  • Jagoran na Kwankwasiyya bai halarci taron NEC na jam'iyyar ba wacce ke fama da rikicin cikin gida

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihar Kano, Hashimu Dunguruwa, ya bayyana labarin dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin labarin ƙarya.

Da yake magana da jaridar Nigerian Tribune ta wayar tarho a birnin tarayya Abuja, Dunguruwa ya bayyana cewa yana wajen taron shugabannin jam'iyyar kuma ba a dakatar da jagoran na Kwankwasiyya ba.

NNPP ta musanta dakatar da Kwankwaso
Shugaban NNPP ya musanta cewa jam'iyyar ta dakatar da Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ba a dakatar da Kwankwaso ba

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kwamitin Amintattu Na NNPP Ya Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam'iyyar, Bayanai Sun Fito

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yanzu haka ina Abuja inda shugabannin jam'iyya ke gudanar da taro, babu wani abu dangane da dakatarwar."
"Muna wajen taron majalisar zartaswa ta ƙasa (NEC) ta jam'iyyar a Abuja, yanzun nan mu ka kaɗa ƙuri'ar amincewa da Kwankwaso."

Ya kuma ƙara da cewa majalisar zartaswar ta ƙara wa'adin shugaban riƙo na jam'iyyyar da sakataren jam'iyyar.

Shugaban ya ƙara da cewa gwamnan jihar Kano, sanatoci da ƴan majalisun tarayya sun goyi bayan taron na NEC tare da kaɗa ƙuri'ar amincewa da Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso bai halarci taron NEC ba

Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa bai halarcin taron NEC na jam'iyyar ba da aka yi a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton Daily Trust.

An gudanar da taron ne dai domin tabbatar da korar shugaban kwamitim amintattu na jam'iyyar, Dr Boniface Aniebonam, sakataren watsa labarau na jam'iyyar, Dr. Agbo Major da wasu mutum 14

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Jam'iyyar NNPP ta yi fama da rikice-rikice cikin ƴan kwanakin nan yayin da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa ya kori wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Jigon NNPP Ya Fice Daga Jam'iyyar

A wani labarin kuma, jigon jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Ben Angwe ya tattara ƴan komatsansa ya fice daga jam'iyyar.

Ben Angwe ya bayyana cewa rikic da hargitsin da jam'iyyar ke ciki ne suka sanya dole ya haƙura da zama a cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng