Gwamna AbdulRazaq Ya Fatattaki PPS, Ya Kori Dukkan Hadimansa daga Aiki
- Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya runtuma kora a wani mataki na aiwatar da sauye sauye ga harkokin gudanar da mulkinsa
- Wannan sallamar aiki ta shafi dukkan masu ba da shawara na musamman, manyan mataimaka da kuma mataimakin shugaban ma’aikata
- Gwamnatin jihar Kwara ta ce gwamnan ya dauki matakin ne don ba karin ‘yan jam’iyya dama da kuma kawo sabon kuzari a tafiyar da mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da wani sabon sauyi a cikin gwamnatinsa wanda ya shafi masu ba shi shawara da manyan mataimaka.
Sauyin ya shafi dukkan masu bada shawara na musamman, masu ba da shawara, manyan mataimaka, mataimaka na musamman, da kuma mataimakin shugaban ma’aikatan gwamna da babban sakataren sirri na gwamna.

Source: Twitter
Dalilin gwamna na korar hadimansa
Mataimakin babban sakataren yada labaran gwamna, Mashood Agboola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya kira matakin da “karamin sauyin tsari a majalisar gwamna” in ji rahoton Premium Times.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne domin bai wa karin mambobin jam’iyyar APC damar shiga harkokin gwamnati tare da kawo sabon kuzari wajen gudanar da ayyuka.
A cewar sanarwar, sauyin ya shafi:
- Masu ba da shawara na musamman ga gwamna
- Masu ba da shawara
- Manyan mataimakan gwamna
- Mataimaka na musamman
- Mataimakin shugaban ma’aikatan gwamna
- Babban sakataren sirri na gwamna
Dalilin gamna na sallamar hadimansa
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana godiyarsa ga jami’an da sauyin ya shafa saboda irin hidimar da suka yi wa jihar.
Ya kuma yi musu fatan alheri a sauran ayyukan da za su gudanar a gaba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito a safiyar Litinin.
Sanarwar ta ce:
"Wannan mataki wanda aka dauka domin ba wasu 'yan jam'iyyar damar samun mukamai da kuma sanya sababbin jini a aikin gwamnati, ya kuma shafi mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnati da PPS ga gwamna.
"Gwamna ya na mika godiya ga dukkan wadanda wannan kora ta shafa bisa irin kokarin da suka yi na yiwa jiha hidima. Ya na yi masu fatan alheri a ayyukansu na gaba."

Source: Original
Umarnin da aka ba wanda aka kora
Haka kuma, gwamnan ya umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Gwamnatin Kwara ta ce wannan sauyin na daga cikin kokarin sake tsara wasu bangarori na tawagar gwamnati da kuma fadada damar shiga harkokin mulki.
Matakin ya zo ne yayin da gwamnatin AbdulRazaq ke kokarin kara karfafa tsarin tafiyar da mulki tare da shigar da sababbin masu jini a jika cikin ayyukan gwamnati.
Gwamna ya zabi wanda zai gaje shi
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana wanda yake goyon bayan ya zama magajinsa a zaben da za a yi a farkon 2027.
AbdulRazaq, wanda wa'adinsa na biyu zai kare a 2027, ya zabi Abdulfatai Yahaya Seriki a matsayin dan takarar gwamnan da yake goyon baya a APC.
Wannan mataki da gwamnan ya dauka na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar APC ke fama da rikicin cikin gida tun bayan fara zabukan fitar da gwani.
Asali: Legit.ng

