Sanata Barau Ya Gwangwaje Dalibai Sama da 600 da Tallafin Karatu a Kano

Sanata Barau Ya Gwangwaje Dalibai Sama da 600 da Tallafin Karatu a Kano

  • Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin ya bai wa ɗaliban jami'ar BUK 628 tallafin karatu
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce za a faɗaɗa shirin tallafin domin kowane ɗalibi a mazaɓarsa ya amfana
  • Kakakin sanata Barau ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Sanatan ya ba da tallafi ba a mazaɓar Kano ta arewa

Kano state - Sanata Barau Jibrin mai wakiltar mazabar Kano ta arewa a majalisar dattawa ya bayar da tallafin karatu ga dalibai 628 na Jami’ar Bayero da ke jihar Kano (BUK).

Daliban, waɗanda aka zaƙulo daga mazabar Kano ta Arewa, mataimakin shugaban Sanatocin yan ba kowane ɗaya Naira 50,000, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Sanata Barau Ya Gwangwaje Dalibai Sama da 600 da Tallafin Karatu a Kano Hoto: Senator Barau Jibrin
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, shi ne ya jagoranci kaddamar da fara bada tallafin karatun a tsangayar ilimi ta BUK.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Zata Ɗauki Sabbin Ma'aikata 300,000 a Faɗin Najeriya, Sahihan Bayanai Sun Fito

Ya ce Sanata Barau ya kirkiro shirin domin tallafa wa al’ummar mazabarsa su samu damar ci gaba da karatunsu a manyan makarantun kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barau zai tallafa wa kowane ɗalibi a mazaɓarsa

Haka zalika a wata sanarwa da mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir ya fitar, ya ce za a faɗaɗa tsarin tallafin karatun.

Ya bayyana cewa za a faɗaɗa wannan tallafin ta yadda kowane ɗalibin mazaɓar Kano ta Arewa da ke karatu a manyan makarantun ƙasar nan zai amfana.

A rahoton Leadership, Mudashir ya ce:

"Wannan karimcin ba na daliban BUK ba ne kawai, duk dalibin mazaɓar Kano ta Arewa da ke karatu a Najeriya zai ci gajiyar wannan shiri."
"Ba wannan ne karon farko ba, ya saba yin irin wannan tallafin. Ya kuma bai wa manoma irin wannan tallafi, da sauransu a mazaɓarsa.”

Kara karanta wannan

"Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Shiga Ruɗani" Atiku Ya Ƙara Bankaɗo Abinda Tinubu Ya Yi a 1999 da 2023

Ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan damar su dage wajen karatu domin cika burinsu na neman ilimi.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, Adama Iliyasu Rabiu, dalibi da ke matakin 400 Level, ya godewa Barau bisa wannan karimcin da aka yi masa, tare da addu’ar Allah ya saka masa.

'Yan Daba Sun Kai Hari Babbar Sakatariyar Jam'iyyar LP a Jihar Imo

A wani labarin kuma Wasu 'yan daba sun kai farmaki sakatariyar jam'iyyar Labour Party da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Yayin harin, 'yan daban sun rushe ginin Sakatariyar LP wacce ke kan titin Wethedral kusa da tsohuwar kasuwar katako a Owerri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel