Jerin Ministocin da Har Yau Shugaba Tinubu Bai Nada Ba da Dalilai

Jerin Ministocin da Har Yau Shugaba Tinubu Bai Nada Ba da Dalilai

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 ranar Litinin 21 ga watan Agusta, 2023, adadi mafi yawa a nahiyar Afirka kuma karo na farko a tarihin Najeriya tun 1999.

Tun da farko, majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da naɗin ministocin bayan shugaban ƙasar ya tura sunayen mutane 48.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Jerin Ministocin da Har Yau Shugaba Tinubu Bai Nada Ba da Dalilai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jerin ministocin da majalisa ba ta amince da su ba har yanzu

Haka nan kuma majalisar dattawan ta dakatar da amincewa da sunayen mutum uku a matsayin ministoci, ta ce hakan ya faru ne saboda wasu dalilan tsaro, inji rahoton Vanguard.

Ministocin da majalisar ta ƙi aminta da naɗinsu sun haɗa da, Malam Nasiru El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Abubakar Ɗanladi, tsohon mataimakin gwamnan Taraba da Stella Okotete daga jihar Delta.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Abun Alkairin da Zai Faru Kan Man Fetur a Karshen 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan lamari dai ya taimaka wajen barin wasu ma'aikatu babu ministoci duk da shugaban ƙasa Tinubu ya kafa majalisar zartarwansa.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin ma'aikatun da har kawo yanzu babu ministoci, ga su kamar haka

Ma'aikatar matasa

Da farko shugaban ƙasa Tinubu ya tura Injiniya Momoh zuwa ma'aikatar matasa a matsayin ministan matasan Najeriya amma daga baya kuma ya canja masa wurin aiki.

Tinubu ya maida Injiniya Momoh zuwa ma'aikatar Neja Delta awanni 24 kacal gabanin rantsar da ministoci.

Sakamakon haka ma’aikatar ta ci gaba da zama ba bu minista duk kuwa da yadda shugaban kasa ya ba da muhimmanci ga ci gaban matasa da kuma jawo su cikin harkokin shugabanci.

An bayar da shawarwari da dama musamman daga bangaren ƙungiyoyin jam’iyyar APC kan wanda ya dace da wannan mukamin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Minista 1 Kan Muhimmin Batu a Villa, Bayanai Sun Fito

Ma'aikatar muhalli

Duk da cewa an nada Ishaq Salako a matsayin karamin ministan muhalli, har yanzu shugaban kasar bai bayyana wani babban ministan muhalli ba.

Yayin rabawa ministocin wurin aiki, fadar shugaban kasar ta ce an kebe mukamin ne ga Kaduna, lamarin da ke nuni da cewa El-Rufai zai maye gurbin da zarar majalisar dattawa ta amince da shi.

Da yake zantawa da Legit.ng Hausa kan haka, Honorabul Richard Ngene, jigon APC ya ce ragowar ministocin biyu suna da matuƙar muhimmanci ga nasarar Tinubu.

A kalamansa ya ce:

"Ma'aikatun biyu da ake magana a kai suna da matuƙar muhimmanci sosai, kuma ya kamata a ba da lokaci don nada mutane masu gaskiya da za su jagoranci al'amuransu."

An Zabi Dan Shekara 53 a Matsayin Sabon Sarki a Jihar Oyo

A wani rahoton kuma Masu naɗa sarki a Masarautar Iseyin sun zaɓi Prince Olawale Oyebola a matsayin sabon Sarki ranar Talata, 29 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Shugaban Fitacciyar Jam'iyya Na Ƙasa, Ta Bayyana Sunan Sabon Shugaba

Mambobin majalisar naɗa Sarkin sun isa fadar masarautar da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata bayan jami'an tsaro sun kewaye Masarautar domin tabbatar da doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262