Karatun Tinubu: Ya Kamata Yan Najeriya Su Shiga Rudani Kamar Ni, Atiku Abubakar

Karatun Tinubu: Ya Kamata Yan Najeriya Su Shiga Rudani Kamar Ni, Atiku Abubakar

  • Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake yin kalaman shaguɓe kan takardun karatun shugaban ƙasa, Bola Tinubu
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce a tunaninsa kowane ɗan Najeriya mai hankali kansa ya kulle kan bayanan karatun Tinubu
  • A cewar Atiku, tarihin karatun da Tinubu ya gabatar a 2023 ya sha bamban da na shekarar 1999

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ƙara yin isgili ga tarihin karatun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Atiku, ɗan taƙarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023 da ya gabata, yana kalubalantar takardar shaidar kammala digirin da jami'ar jihar Chikago a Amurka ta bai wa Tinubu.

Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa.
Karatun Tinubu: Ya Kamata Yan Najeriya Su Shiga Rudani Kamar Ni, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Ya ce takardun karatun shugaban ƙasa mai ci, Bola Tinubu, suna tattare da kokwanto da ruɗani mai girma.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

A wani rubutu da ya wallafa a shafin X (watau Tuwita), Atiku ya zargi Tinubu da tsallake karatun Firamare da Sakandire, ya wuce kai tsaye zuwa jami'ar Chicago ta ƙasar Amurka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, a shekarar 1999, Tinubu ya yi ikirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John’s, Aroloya da ke jihar Legas, kafin ya wuce makarantar kananan yara a Ibadan.

Bayanan karatun Tinubu sun bambanta

Ya yi zargin cewa tarihin karatun Shugaba Tinubu a 2023 ya bambanta da wanda aka gabatar a shekarar 1999 lokacin da ya tsaya takarar gwamna a jihar Legas.

Atiku ya kara da cewa a wannan karon, shugaban kasa Tinubu ya ce ya halarci jami’ar jihar Chicago ne kawai ba tare da karatun firamare da sakandare ba.

Ya ce:

“Na farka da safiyar yau ina mamakin yadda zamani ya kawo mu, a ce a shekarar 1999, Tinubu ya yi ikirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John, Aroloya da ke Legas, da kuma makarantar yara a Ibadan.”

Kara karanta wannan

Atiku Ya Samo Makamar Kwace Mulkin Tinubu, Ya Gano Tsaiko a Bayanan Shugaban Kasar Na 1999 da 2023

"A cewarsa, mataki na gaba da ya taka a neman ilimi shi ne Kwalejin Gwamnati ta Ibadan, jihar Oyo da Kwalejin Richard Daley da kuma Jami’ar jihar Chicago ta ƙasar Amurka."
"Abin mamaki, a wannan shekarar 2023, Tinubu ya tsaya kan cewa ya halarci jami'ar Chicago (@ChicagoState) ne kaɗai. Kaina ya kulle. Ta yaya hakan zai yiwu?"

A ganina yan Najeriya na cikin ruɗani - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ci gaba da cewa:

"Ina tunanin cewa duk ’yan Najeriya masu hankali ya kamata su shiga ruɗani kamar yadda na yi duba da bayanan Tinubu na cewa bai yi karatun Firamare da sakandare ba, duk da haka yana da digiri na jami’a."
"Zamu so mu tambayi Tinubu yadda ya samu wannan nasarar domin mu yi koyi da hazakarsa."

Bayan kammala zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jigon APC Ya Yi Hasashen Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke

Amma bayan haka, Atiku ya ƙalubalanci nasarar APC a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa, inda ya bankaɗo alamomin tambaya da dama ciki harda karatun Tinubu.

Hukumar PSC Ta Umarci DIG 4 Su Gaggauta Yin Ritayar Dole

A wani rahoton kuma Gwamnatin shugaba Tinubu ta sallami mataimakan sufetan yan sanda na ƙasa 4 kuma ta maye gurbinsu.

Hukumar PSC ta umarci DIG huɗu, wadanda ke sama da sabon muƙaddashin IGP na ƙasa, su yi ritayar dole, ta sanar da sunayen sabbin da ta naɗa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel