EFCC Za Ta Binciki Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano Da Ke Binciken Kan Bidiyon Dalar Ganduje

EFCC Za Ta Binciki Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa Ta Kano Da Ke Binciken Kan Bidiyon Dalar Ganduje

  • Hukumar EFCC ta bayyana neman shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimingado
  • Hakazalika, CCB ta bayyana bukatar sanin wasu bayanai da suke da alaka da kudaden da aka kwata daga masu laifi
  • A baya, Rimingado ya bayyana aniyar tabbatar da bankado dalilin da yasa Ganduje yake sankama daloli a babbar riga a baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da kuma ta kula da da’a (CCB) na tuhumar Muhyi Rimingado bisa zargin almundahana.

Yayin da wata wasika da EFCC ta fitar ta bukaci shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Rimingado, da ya tura daraktan kudi na PCACC su bayyana a hedkwatarta da ke Abuja ranar 29 ga watan Agusta, CCB ta bukaci ya ba ta wasu takardu.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

Dukkan hukumomin tarayyar biyu sun nemi shugaban na PCACC da ya ba su bayanan kudi da cikakkun bayanai na dukiyar da hukumar ta kwata, Peoples Gazette ta tattaro.

Mai bincike kan Ganduje zai fuskanci tuhumar EFCC
EFCC na neman Muhyi Rimingado | Hotuna: Abdullahi Umar Ganduje, Economic and Financial Crime Commssion, Barr. Muhuyi Magaji Rimingado
Asali: Facebook

Bayani daga EFCC kan Rimingado

A cewar sanarwar ta EFCC:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duba da abubuwan da ke sama, ana rokon ku da ku saki rahoton daraktan kudi da asusun ajiyarku don tattaunawa da wadanda suka dace ta hannun shugaban tawagar AFF/TC da ke Plot 301/302 Cibiyar Bincike da ke Jabi, kan titin filin jirgin sama, Abuja a ranar Litinin, 29 ga Agusta, 2023 da misalin karfe 10:00 na safe.”

Wasikar ta bayyana bukatar sanin kudaden da aka saki ga hukumar tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021 da kuma inda aka kashe kudaden a tsawon shekarun.

Hakazalika, ana bukatar sanin adadin kadarori da kudaden da hukumar ta kwato a hannun wadanda ake zargi da wadanda aka gurfanar tsakanin 2016 zuwa yau, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa: Shin Masu Yi Wa Kasa Hidima Na Iya Zama Minista? Falana, Sauran Lauyoyi Sunyi Martani

Alakar Rimingado, Ganduje da Abba Gida-Gida

A shekarar 2022, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya kori Rimingado bisa zarginsa da laifin cin zarafin aikinsa na ofis.

Amma a ranar 21 ga watan Yuni, sabon gwamnan jihar, Abba Yusuf ya sake amincewa da mayar da shi a matsayin shugaban hukumar ta PCACC.

Rimingado ya sha alwashin zai binciki wani faifan bidiyon da ya nuna yadda Ganduje yake sankama damman daloli a babbar riga; zargin da ake na rashawa ne.

Ganduje ya biya Rimingado hakkokinsa

A bangare guda, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya biya tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen jama'a ta jihar, Muhuyi Rimin Gado hakkokinsa na sama da naira miliyan 5 a kotu, jaridar Aminiya ta rahoto.

Tun farko dai Rimin Gado ya shigar da karar gwamnatin Ganduje gaban kotu inda ya nemi a biya shi hakkokinsa bayan tsige shi daga kan kujerarsa ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Nufin Allah: Dangote ya ci ribar biliyoyi a rana 1, ya sake zama wanda ya fi kowa kudi a Afrika

Bayan nan sai kotun ta umurci gwamnatin Kano ta biya shi hakkokin nasa, da kuma tabbatar da shi a matsayin sahihin shugaban hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel