Siyasar Najeriya
Muƙaddashin shugabam PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa zaben da tsagin Wike suka shirya na shugabannin jam'iyya a Kudu maso Kudu ya saɓa doka.
Magoya bayan Nasir El-Rufa'i sun i zargin cewa zaman Olu Agunloye a matsayin sakataren SDP zai ba gwamnatin Bola Tinubu damar yi wa jam'iyyar katsalandan.
Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa na LP a zaben da ya gabata na 2023 ya shiga ganawar sirri da Gwamna Bala Muhammed a Bauchi.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi wani jigoɓda ya dawo APC a jihar Oyo. Ya bayyana cewa jam'iyyar za ta kwato Osun, Oyo a hannun PDP.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa rashin naɗa shi minista ne ya tunzura shi ya bar jam'iyyar APC.
Shugabar riko na LP, Sanata Nenadi Usman ta karyata jita-jitar cewa ta fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar SDP mai adawa a Najeriya wanda Nasir El-Rufai ya koma.
Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna damuwa kan hana shi shiga zauren Majalisar Dokokin Jihar Ribas na wucin gadi domin sakw gabatar da kasafin kuɗin 2025.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya gaya wa Buhari shirinsa na barin APC kuma sai da ya amince sannan ya koma SDP.
Jam'iyyar NNPP mai adawa ta harzuka kan kalaman da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin tarayya na da hannu a cikin rikicin da ya addabe ta. Ta ba shi wa'adi.
Siyasar Najeriya
Samu kari