Ana tsakiyar Batun El Rufai, Peter Obi Ya Sa Labule da Gwamna Bala kan Dalilai Masu Karfi
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi ya kai ziyara jihar Bauchi domin batun siyasa da mulki
- Mista Obi ya yi ganawar sirri da Gwamna Bala Muhammed, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi
- Wannan ganawa dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan sauya shekar Malam El-Rufai daga APC zuwa SDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 karkashin inuwar jam'iyyar LP, Mista Peter Obi ya kai ziyara ta musamman jihar Bauchi.
Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya shiga ganawar sirri yanzu haka da Gwamna Bala Mohammed a gidan gwamnatin Bauchi.

Asali: Twitter
Tashar Channels tv ta tattaro cewa har kawo yanzu babu wata sanarwa kan maƙasudin wannan ziyara ta Obi amma ana hasashen dalilai ne masu ƙarfi.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da Peter Obi, gwamnan Bauchi ya bayyana shirin kifar da Tinubu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya gana da Gwamna Bala Mohammed
Sai dai ana tsammanin Peter Obi da gwamnan Bauchi za su yi wa manema labarai jawabi bayan sun fito daga taron wanda ke gudana a sirrance yau Alhamis, 13 ga watan Maria, 2025.
Ganawar da aka yi tsakanin jigon LP da gwamnan jam'iyyar PDP na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa suka fara kankama gabanin babban zaben shekarar 2027.
Sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2023
Peter Obi shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasa na 2023 wanda tsohon gwamnan Lagos, Sanata Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya samu nasara.
Shugaba Tinubu ya lashe zaɓen ne daga cikin ƴan takara 12 da suka fafata a watan Fabrairun, 2023, inda ya samu kuri'u kusan nunkin Atiku Abubakar, wanda ke mara masa baya.
Tinubu ya samu kuri'u 8,794,726 a zaɓen yayin da wazirin Adamawa ya zo na biyu da ƙuri'u 6,984,520, sai kuma Peter Obi da ya take masu baya da ƙuri'u 6,101,533.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya zo na hudu, ya samu nasara a jiharsa ta Kano. Ya samu kuri'u 1,496,687.

Asali: Twitter
Shin Peter Obi zai haɗa kai da Gwamna Bala?
Bayan haka ne jam'iyyun adawa suka fara yunkurin haɗa kai domin kawar da APC daga gadon mulkin Najeriya a zaɓen 2027.
An ga Atiku Abubakar tare da Peter Obi, sannan kuma ya gana da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, lamarin ya sa jita-jitar za su haɗe ta ƙara karfi.
Ana ganin dai wannan ziyara da Obi ya kai wa gwamnan Bauchi ba za ta rasa nasaba da batun siyasar 2027 ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Atiku ya musanta sauya sheka daga PDP
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce yana nan daram a jam'iyyar PDP, kuma ba shi da shirin sauya sheka.
Alhaji Atiku ya bayyana rahotannin da ke cewa yana shirin barin PDP a matsayin ƙarya maras tushe ballantana kuma makama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng