SDP Ta Yi Babban Kamu, Mai Koyi da Buhari, MC Tagwaye Ya Hade da El Rufa'i
- Fitaccen mai koyi da shugaba Muhammadu Buhari, MC Tagwaye ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP
- Yayin sauya sheka, MC Tagwaye ya zargi APC da rashin biyayya ga manufofinta na farko da kuma rashin damawa da matasa
- Haka zalika ya kara da cewa SDP na da kyakkyawar manufa da ke ba da fifiko ga dimokuradiyya da ci gaban ‘yan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shahararren mai barkwanci kuma dan siyasa, Obinna Simon wanda aka fi sani da MC Tagwaye, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP.
Ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan watanni na tunani mai zurfi da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan
An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, MC Tagwaye ya ce APC ta kauce daga manufofinta na farko kuma ba ta damu da jin dadin ‘yan kasa ba, don haka ya yanke shawarar barinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ficewar MC Tagwaye daga APC
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 14 ga Maris, 2025, MC Tagwaye ya bayyana cewa APC ba ta da tsarin da ke mutunta mambobinta masu biyayya.
MC Tagwaye ya ce:
“APC ta rasa kyakkyawan tsarin saka wa masu biyayya da kuma kyale tsirarun manya su rika juya akalar jam’iyya ba tare da la’akari da ra’ayin mafiya rinjaye ba.”
Hakazalika, ya zargi jam’iyyar da daukar matakan da ke jefa talakawa cikin wahala, lamarin da ya kara tabbatar masa da cewa lokaci ya yi da zai yi bankwana da APC.
Ya kara da cewa jam’iyyar ba ta da cikakken tsarin dimokuradiyya, domin wasu ‘yan tsiraru ne ke yanke hukunci a madadin jam’iyya gaba daya.

Asali: UGC
SDP ta zama mafita a Najeriya – Tagwaye
MC Tagwaye ya ce ya yanke shawarar komawa SDP ne saboda jam’iyyar na da tsari mai kyau da ke bai wa matasa damarmaki.
Ya ce:
“SDP ta zama haske a cikin duhu. Jam’iyyar na da tsayayyen tsari na gaskiya da adalci, sannan tana da manufa ta ciyar da kasa gaba.”
A cewarsa, SDP na ba ‘yan Najeriya damar fadin albarkacin bakinsu tare da taka rawar gani a dimokuradiyya.
MC Tagwaye ya ce ya riga ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban mazabarsa a APC, wanda ke nuna cewa ya rabu da jam’iyyar har abada.
Ya ce yana fatan yin aiki tare da SDP don ganin an samar da sabuwar Najeriya da ke jin dadin kowa.
MC Tagwaye ya yi kira ga ‘yan Najeriya
Da yake kammala sanarwarsa, MC Tagwaye ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai domin tabbatar da sauyi a kasa.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a yi aiki tare domin gina makoma mai kyau ga Najeriya da al’ummarta.
Hamza Al-Mustapha ya koma SDP
A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya koma SDP.
Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa Manjo Hamza Al-Mustapha ya sauya sheka ne a yammacin ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng