"Ba Mu Yarda ba," El Rufai Ya Ƙara Shiga Matsala bayan Komawa SDP, Matasa Sun Masa Rubdugu

"Ba Mu Yarda ba," El Rufai Ya Ƙara Shiga Matsala bayan Komawa SDP, Matasa Sun Masa Rubdugu

  • Matasan SDP sun yi fatali da sauya shekar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun ce ya shigo jam'iyyarsu ne da wata manufa
  • Shugaban kungiyar matasan SDP na ƙasa, Kwamared Abdulsamad Bello ya ce babu wani alheri da jam'iyyar za ta samu saboda zuwan El-Rufai
  • Ya zargi tsohom gwamnan da yunƙurin kwace shugabancin SDP, yana mai cewa kowa ya san halin El-Rufai na murƙushe ƴan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙungiyar matasan jam’iyyar SDP ta Najeriya ta yi watsi da sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Matasan sun nuna rashin gamsuwa da shigowar El-Rufai cikin SDP, su na zarginsa da ƙoƙarin mamaye jam'iyyar domin biyan buƙatun kansa.

Malam Nasiru.
Matasan SDP sun yi fatali da sauya sheƙar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @Elrufai
Asali: Twitter

El-Rufai ya fice daga APC a ranar Litinin bayan watanni yana tattaunawa da manyan jiga-jigan ‘yan adawa, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

SDP ta tono 'makarkashiyar' da gwmanatin APC ke shiryawa El Rufai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan SDP ba su yarda da El-Rufai ba

Sai dai da yawa daga cikin ƴan SDP musamman matasa ba su gamsu shigarsa jam'iyyar ba, suna ganin ya haɗe da su ne domin cimma burinsa na siyasa.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar matasan SDP, Kwamared Abdulsamad Bello, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce El-Rufai bai cancanci shiga SDP ba ta fuskar ɗabi’a da siyasa.

"Ba mu yarda da shigowar El-Rufai cikin jam'iyyarmu ba. Ba ya shigo domin ya inganta ta ba ne, sai don ya rusa jam'iyya kafin ta samu damar girma," in ji Bello.

Matasa sun caccaki shugabannin SDP

Ƙungiyar matasan ta kuma soki shugabancin SDP bisa abin da suka kira "yarjejeniya ta ɓoye" da ta bai wa El-Rufai damar shiga jam’iyyar.

Shugaban ƙungiyar matasan ya yi gargadin cewa zuwan Malam Nasiru na iya haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin ƴaƴan SDP.

"El-Rufai bai taɓa yarda da dimokraɗiyya ba. Tarihinsa na murƙushe ‘yan adawa, watsi da ra’ayin mambobi, da amfani da ƙarfin iko ba ɓoyayye ba ne, kowa ya sani," in ji shi.

Kara karanta wannan

Siyasa mugun wasa: El Rufa'i na fatan Atiku da Obi su hade da shi a SDP

Bayan shiga SDP, a ranar Laraba, wasu magoya bayan El-Rufai sun gudanar da zanga-zanga a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, suna kira ga sakataren jam’iyyar na ƙasa, Olu Agunloye, da ya sauka daga mukaminsa.

El-Rufai ya fara fuskantar kalubale a SDP

A cewar ƙungiyar matasan SDP, wannan wata alama da ke nuna shirin El-Rufai na ƙwace shugabancin jam’iyyar, rahoton Vanguard.

"Kwanaki kaɗan bayan shigowarsa, El-Rufai ya fara ƙoƙarin sauya shugabancin jam’iyyar. Ya matsa wa Olu Agunloye ya yi murabus, maimakon bin tsarin SDP," in ji sanarwar.

Matasan sun kuma zargi El-Rufai da amfani da SDP domin ceto kansa daga matsalar siyasa, musamman bayan da ya fara sukar shugaba Bola Tinubu da APC.

Wani mai goyon bayan El-Rufai a Kaduna, Ibrahim Ya'u, ya ce kamata ya yi duk wani ɗan SDP ya yi murna da sauya sheƙar Malam Nasiru.

Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa SDP ta ƙara karfi da karbuwa a wurik ƴan Najeriya tun da Malam El-Rufai ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kalaman El Rufa'i sun tada ƙura, ƴan sanda sun yi magana kan zargin 'sace kwamishina'

"A zahirin gaskiya matasan SDP da suka yi wannan maganar ba su san waye Malam ba, zuwansa alheri ne ga jam'iyyar kuma idan suka yi haƙuri za su gani," in ji shi.

Adebayo ya ayyana shirinsa na takara a SDP

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan takarar SDP a zaben shugaban ƙasa na 2023, Adewole Adebayo, ya jaddada aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

A wata hira da aka yi da shi bayan sauya sheƙar El-Rufai, Adebayo ya ce SDP ba ta shiga wata tattaunawa ta haɗakar jam'iyyun siyasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng