2027: Gwamna Uba Sani Ya Samu Tagomashi a Shirinsa Na Tazarce

2027: Gwamna Uba Sani Ya Samu Tagomashi a Shirinsa Na Tazarce

  • Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na Najeriya (ALGON), reshen jihar Kaduna ta nuna goyon bayanta ga Gwamna Uba Sani
  • Shugaban ALGON na jihar Kaduna ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya taimaka musu wajen lashe zaɓensu da aka yi
  • Honorabul Jamilu Albani ya nuna cewa za su rama biki domin tabbatar da cewa gwamnan ya samu ƙuri'u masu yawa a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na Najeriya (ALGON), reshen jihar Kaduna, Hon. Jamilu Albani, ya tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Gwamna Uba Sani.

Shugaban ya ƙara da cewa dukkan shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Kaduna sun himmatu wajen maida biki ga Gwamna Uba Sani kan taimakon da ya yi musu suka lashe zaɓe.

Gwamna Uba Sani ya samu goyon baya
Kungiyar ALGON ta goyi bayan Uba Sani a 2027 Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jamilu Albani ya yi wannan bayanin ne lokacin da Gwamna Uba Sani ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙananan hukumomi 23 da mataimakansu a daren Laraba domin yin buɗa baki, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana alfarmar da Tinubu ya nema a wajensa gaban duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ALGON za ta marawagwamna Uba Sani baya

Shugaban na ALGON, wanda kuma shi ne shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, ya bayyana cewa wasu ƴan adawa na sukar Gwamna Uba Sani ne saboda ya goya musu baya.

"Amma da ikon Allah Madaukakin Sarki da kuma goyon bayan mai girma Gwamna, an zaɓe mu a matsayin shugabannin ƙananan hukumomi."

- Jamilu Albani

Jamilu Albani ya ƙara da cewa ko bayan zaɓensu, Gwamna Uba Sani ya basu ƴancin tafiyar da harkokin ƙananan hukumominsu ba tare da yi musu katsalandan ba.

Ya bayyana cewa gwamnan yana tallafa musu a siyasance, inda ya ƙara da cewa ya biya jami’an jam’iyya haƙƙoƙinsu kuma yana rabawa al’umma tallafi.

"Gwamnatin da ta gabata ba ta kula da jami’an jam’iyya a matakin ƙananan hukumomi ba, domin a duk tsawon mulkinta, kowannensu bai samu fiye da N9,000 ba."
"Saboda haka, a 2027, za mu maida wannan alheri ta hanyar tabbatar da cewa jama’armu sun kaɗa ƙuri'u sosai ga Gwamna Uba Sani."

Kara karanta wannan

Bayan ficewar El Rufai, Ganduje ya fadi shirin APC na kwace jihohi 2 a hannun PDP

"Ƴan adawa da ke tunanin za su iya kayar da Gwamna Uba za su fuskanci rashin nasarar da ba su taɓa gani ba a rayuwarsu."

- Jamilu Albani

Gwamna Uba Sani ya ba da shawara

Yayin da yake jawabi a wajen buɗa bakin, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ƙananan hukumomi suna da matuƙar muhimmanci a siyasa domin sune matakin gwamnati mafi kusa da jama’a.

"Ƙaramar hukuma ita ce tushen siyasa, kuma ina ba ku shawara ku aiwatar da ayyukan ci gaba, ku taimakawa jama’a a lokacin da suke da buƙata, sannan ku raba musu abin da kuke da shi."

- Gwamna Uba Sani

Tsofaffin ma'aikata sun ba Uba Sani wa'adi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsofaffin ma'aikatan da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Kaduna.

Tsofaffin ma'aikatan sun buƙaci Gwamna Uba Sani ya biya su haƙƙoƙinsu ko kuma su mamaye gidan gwamnatin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng