Magoya Bayan El Rufa’i Sun Fara Shirin Birkita Jam'iyyar SDP
- Wasu magoya bayan tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i, sun nemi a cire sakataren jam’iyyar SDP saboda shari’ar da yake yi da EFCC
- Sun bayyana bukatar ne kwanaki kadan bayan El-Rufa'i ya watsar da APC saboda dalilan sauka daga turbar da aka kafa jam'iyyar
- Lauyan SDP na kasa, Aderemi Abimbola, ya yi martani a kan bukatar, ya ce babu dalilin da za su wargaza kwamitin gudanarwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Kasa da sa’o’i 48 bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sauya sheka zuwa SDP, magoya bayansa sun bukaci a sake duba kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa.
Tawagar da ke goyon bayan tsohon gwamnan ta bayyana cewa akwai bukatar a cire sakataren jam’iyyar na kasa, Olu Agunloye.

Asali: Facebook
Wani rahoto da ya kebanta da jaridar The Guardian, magoya bayan El-Rufa'i na ganin shari’ar da ake yi da Agunloye a gaban hukumar EFCC na iya ba gwamnatin tarayya damar yin katsalandan a harkokin SDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufa'i: SDP ta musanta karbar sababbin 'ya 'ya
Lauyan SDP na kasa, Aderemi Abimbola, ya bayyana cewa, akasin rade-radin da ke yawo cewa 'yan APC da PDP suna tururuwa zuwa jam'iyya, ya ce har yanzu El-Rufai ne kadai ya shige ta.
Sai dai ya bayyana cewa tun farkon wannan shekara, jam’iyyar ta karbi wasu ‘yan siyasa da suka sauya sheka daga jihohi daban-daban na Arewacin Najeriya.

Asali: Facebook
Abimbola ya kara da cewa kuma har yanzu, suna ci gaba da tattaunawa da wasu da ke sha’awar shiga jam’iyyar.
Ya ce:
“Jiya ma, wasu manyan magoya bayan APC daga Gombe sun zo nan. Wadannan na daga cikin muhimman mutane a yakin neman zaben gwamnan jihar.
Lamarin ya kai ga cewa da gwamnan ya gan su a cikin jirgin sama, ya fusata matuka har ya so ya mare daya daga cikinsu.”
Jam'iyyar SDP ta yi maraba da El-Rufai
Abimbola ya bayyana cewa sauya shekar El-Rufa'i zuwa SDP babbar nasara ce ga jam’iyyar, tare da jaddada cewa tsohon gwamnan na da ginshikin siyasa mai karf.
Ya ce tasirin Nasir El-Rufa'i ba a jihar Kaduna kawai ya tsaya ba, har da sauran muhimman wurare a Arewacin kasar da Najeriya baki dayanta.
Aderemi Abimbola ya ce:
“Kafin ma ya sanar da sauya shekar sa, magoya bayansa sun riga sun fara shiga jam’iyyar. Shigowarsa zai kara wa SDP karfi matuka.”
Dangane da bukatar sauya fasalin kwamitin gudanarwar jam’iyyar, Abimbola ya ce:
“Babu wani gurbi a kwamitinmu gudanarwarmu, kuma babu wanda zai shiga SDP da burin samun tikitin takara kai tsaye.
Kowanne dan takara sai ya tsaya takara a zaben fitar da gwani. Dole masu sauya sheka su fahimci cewa suna shiga ne a matsayin ‘yan jam’iyya kamar kowa.”
Rikici ya kunno cikin jam'iyyar SDP
A wani labarin, kun ji cewa Kasa da ‘yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauya sheka zuwa SDP, rikici ya barke a tsakanin 'ya'yanta reshen jam’iyyar na jihar Kogi.
Shugaban SDP a jihar, Moses Peter Oricha, ya fitar da sanarwa, ya na kira ga jama’a da hukumomin tsaro da su yi watsi da wani gangami da wasu ke shirin gudanarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng