Bayan Ganawa da Peter Obi, Gwamnan Bauchi Ya Bayyana Shirin Kifar da Tinubu a 2027
- Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce a shirye yake ya hada kai da Peter Obi domin karfafa siyasar adawa gabanin zaben 2027
- Gwamnan ya ce zai hada kai da Obi ne saboda tsohon gwamnan na Anambra yana da hangen nesa da sanin makamar shugabanci
- A nasa bangaren, Obi ya ce ya ziyarci Bala Mohammed a yunkurinsa na tuntubar manyan ‘yan siyasa domin magance matsalolin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi ya bayyana shirin yin aiki tare da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, domin karfafa siyasar adawa gabanin zaben 2027.
Mun ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da Peter Obi a fadar gwamnatin jihar Bauchi, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

Asali: Twitter
Gwamnan Bauchi ya kambama Peter Obi
A yayin wannan ziyara, gwamnan ya mutunta salon siyasar tsohon gwamnan na Anambra, wanda ya kira mai hangen nesa game da shugabanci, inji rahoton Vangaurd.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yana da hangen nesa mai zurfi kan inda ya kamata siyasa da ‘yan siyasa su kasance wajen samar da nagartaccen shugabanci da inganta rayuwar al’umma.
“Kullum jin ra’ayinsa abu ne mai kyau saboda iliminsa mai zurfi da kuma iya amfani da alkaluma wajen fassara abubuwa."
- Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan ya ce tattaunawarsu ta shafi muhimman batutuwan kasa, ciki har da halin da siyasar adawa ke ciki da rikicin da ke faruwa a jihar Ribas.
"Na shirya yin aiki da Obi" - Gwamnan Bauchi
Mai girma, Bala Mohammed ya ce:
“Ina yaba wa abin da yake yi a matsayin jagoran adawa, domin ko muna so ko ba mu so, yanzu shi ne fuskar siyasar adawa a Najeriya."

Kara karanta wannan
'Dan Sule Lamido ya bi sahun mahaifinsa, ya fadi kuskuren ƴan Najeriya a zaben 2023
Ya kuma bayyana cewa yana shirye ya hada kai da Obi domin karfafa adawa mai karfi da tsara hanyoyin kawo ci gaba ga kasa.
“Ina so in bayyana a fili cewa a shirye nake na yi aiki tare da Peter Obi. Dole ne mu hada kai domin kawo shugabanci nagari da samar da adawa mai karfi da tsari.
“Lokaci ya yi da za mu fito da tsare-tsare masu kyau. Wannan hadin gwiwa da muke yi zaburarwa ne ga ‘yan Najeriya, kuma sauran gwamnoni ma na goyon bayan irin wannan hadaka."
- Bala Mohammed.
Peter Obi ya fadi dalilin ziyartar Bala Mohammed

Asali: Twitter
A nasa bangaren, Obi ya ce ziyararsa zuwa Bauchi na daya daga cikin kokarinsa na tuntubar manyan ‘yan siyasa domin tattauna matsalolin kasar.
“Wasu na mamakin dalilin da ya sa na zo Bauchi, to a sani na zo ne domin tattaunawa da Gwamna Bala Mohammed, saboda yana da muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya."

Kara karanta wannan
Abin da Abba Kabir ya fadawa malamai da ya faranta musu rai yayin buda baki a Kano
- Peter Obi.
The Nation ta ruwaito Peter Obi ya jaddada cewa dole ne a magance talauci kafin a iya shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, musamman a Arewacin kasar nan.
A cewar Peter Obi:
“Idan mutane suna magana kan rashin tsaro a Najeriya, musamman a Arewa, ina gaya musu cewa matsalar gaske ita ce talauci. Idana aka ki magance talauci, ba za a iya kawar da rashin tsaro ba."
"Ina fatan ya nemi takara a 2027" - Kwamared Nazir
A zantawarmu da wani matashin dan siyasa a jihar Bauchi, Kwamared Nazir Sanusi Bauchi, ya ce wannan ganawar ba ta zo masu a mamaki ba, domin sun fatan 'Kauran Bauvchi ya nemi takarar shugaban kasa a 2027.
Kwamared Nazir ya ce, gwamnan na Bauchi ya samu kwarewar da zai iya jagorantar Najeriya, la'akari da cewa ya yi minista, ya yi sanata kuma ya yi gwamna.
"Duk wata kwarewa da ake bukata Gwamna Bala yana da ita. Ina da tabbacin Najeriya za ta samu ci gaba da aka ce shi ne ke jagorantar kasar.
"Haduwarsa da Peter Obi, ta nuna cewa shi mutum ne da ke kishin Najeriya, wanda zai iya hada kai da duk wanda yake ganin za su iya kawowa kasar ci gaba."
Ko da aka tambaye shi ra'ayinsa a kan gwamnan ya zama abokin takarar Peter Obi a zaben mai zuwa, Kwamared Nazir ya ce:
"Ka san ita siyasa lissafi ce. Na tabbata idan ya lissafa ya ga cewa zama abokin takarar Peter Obi shi ne mafita ga kasarmu baki daya, zai iya yin hakan."
Matsayar Peter Obi kan takara a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Peter Obi ya bayyana cewa ba lallai sai ya zama shugaban kasa ba, amma burinsa shi ne ganin Najeriya ta inganta.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya yi kira ga matasa da su taka rawar gani wajen samar da shugabanci na gari da zai kawo ci gaba a kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng