Manjo Hamza Al Mustapha Ya Sauya Sheka zuwa SDP, Ya Hade da El Rufa'i

Manjo Hamza Al Mustapha Ya Sauya Sheka zuwa SDP, Ya Hade da El Rufa'i

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Manjo Hamza Al-Mustapha (Mai ritaya) ya koma jam’iyyar SDP a Abuja
  • Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya ce matakin wani sabon shafi ne a siyasar Najeriya
  • Masana sun fara hasashen tasirin sauya shekar Al-Mustapha kan zabukan 2027 da 'yan adawa za su kara da APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon hafsan tsaro na Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (Mai ritaya) ya sanar da shigarsa jam’iyyar SDP.

An karbi Manjo Al-Mustapha ne a wata gagarumar tarba da aka masa a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Al=Mustapha
Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma SDP. Hoto: Shehu Musa Gabam ,SDP National Chairman
Asali: Facebook

Shugaban jam’iyyar, Shehu Musa Gabam, ya wallafa a Facebook cewa matakin wata alama ce ta karfafa siyasar Najeriya bisa tushen adalci, tsaro, da ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman El-Rufai game da komawa SDP, Buhari ya fadi matsayarsa a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SDP ta yi maraba da Manjo Hamza Al-Mustapha

A yayin tarbar Al-Mustapha a hedkwatar SDP, Shehu Musa Gabam ya bayyana cewa shigowarsa jam’iyyar wata babbar dama ce ga ‘yan Najeriya masu neman sabuwar tafiya a siyasa.

Ya ce jam’iyyar SDP na kokarin zama wata babbar kafa ta samar da shugabanci nagari da zai fi mayar da hankali kan bukatun al’umma.

“Zuwan Manjo Dr Hamza Al-Mustapha jam’iyyar SDP wata babbar alama ce ta hadin kai, tsaro, da ci gaban kasa.
"Wannan mataki sabuwar dama ce ga ‘yan Najeriya da ke bukatar shugabanci nagari,”

- Shehu Musa Gabam

Al-Mustapha ya gana da 'yan SDP

Bayan sanar da sauya shekarsa, rahotanni sun nuna cewa Al-Mustapha ya gana da wasu manyan ‘yan siyasa.

An hango tsohon dan takarar shugaban kasar yana gaisawa da 'yan jam'iyyar SDP suna rungumar juna da tafawa da hannu a cikin wani bidiyo.

Kara karanta wannan

Hausawan Legas sun watsar da NNPP, sun koma tafiyar Barau Jibrin a APC

Sauya shekar Al-Mustapha na zuwa ne yayin da ake cewa akwai yiwuwar SDP na shirin kafa kawance da wasu manyan ‘yan siyasa don fuskantar babban zaben 2027.

Tsohon gwamnan Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna da ya koma SDP. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Tasirin Al-Mustapha a siyasar SDP

Al-Mustapha ya taba tsayawa takarar shugabancin kasa a baya, inda ya samu goyon bayan wasu rukunin ‘yan kasa da ke ganin ya dace ya taka rawar gani a harkokin mulki.

A cewar wani mai sharhi a shafin Facebook, Abdulrahman Mohammed Ayas, sauya shekar za ta iya canja tsarin siyasar SDP.

Ya bayyana cewa:

“SDP na kokarin zama babba a siyasar Najeriya, kuma shigowar Al-Mustapha na iya kara wa jam’iyyar farin jini, musamman a tsakanin masu neman shugabanci nagari.”

Shin jam'iyyar SDP za ta yi tasiri a 2027?

Yayin da babban zabe ke kara matsowa, jam’iyyar SDP na kara samun masu ruwa da tsaki da ke shigowa cikinta, wanda hakan na iya zama wata babbar barazana ga manyan jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan

Magoya bayan El-Rufa’i sun fara shirin birkita jam'iyyar SDP

Duk da haka, ana ganin cewa har yanzu akwai bukatar jam’iyyar ta kara aiki tukuru don ganin ta samu goyon bayan al’umma a babban zaben 2027.

Rikici ya bulla a SDP a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban SDP a jihar Kogi ya ce wasu na neman kwace masa ragamar jagoranci.

Shugaban ya yi korafi ne yayin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa SDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng