Jam'iyyar PDP
Jam'iyyu siyasa 40 a Najeriya waɗanda INEC ta soke rijistarsu ta hannu gamayyar jam'iyyu watau CUPP sun ce Atiku da gwamna Okowa ne suka dace da ƙasar nan.
Mai neman zama gwamnan jihar Legas a inuwar jam'iyyar PDP, Mista Jandor, ya gamu da illar yan daba yayin da ya je kamfe karamar hukumar Surulere ranar Jumu'a.
Dino Melaye, kakakin kwamitin yakin zabe na dan takarar shugaban kasa na jam'iyya PDP, Atiku Abubakar ya ce tsohon shugaban kasa, IBB, yana goyon bayan Atiku.
Gwamnatin Jihar Edo za ta rufe duk wani masallac, coci, kulob da gidan cashewa a garin muddin ba su saka na'uarar daidaita sautin da ke fitowa daga cikinsu ba.
Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, ta yanke hukuncin kwace kujarar Sanata daga jihar Akwa Ibom sakamakon sauya sheka daga PDP a shekarar da ta gabata .
Yayin da babban zaɓe ke ta kara matsowa, jam'iyya mai kayan marmari ta kara yin rashi mai girma a jihar Bauchi, kanin ɗan takarar gwamna da wasu sun koma PDP.
Jirgin yakin neman kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya PDP ya garzaya jihar Kebbi, Arewa maso yammacin Najeriya a yau Asabar, 28 ga Junairu
Tawagar gwamnoni 5 da ake wa lakabi da G-5 sun tabbatar da goyon bayansu da masu neman takara a inuwar PDP a jihar Enugu yayin da ake tunkarar babban zabe.
Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP fa sanar da ɗaukar matakin dakatarwa kan shugaban jam'iyya na jihar Ebonyi, Okoroafor, bisa zargin yi mata zagon ƙasa.
Jam'iyyar PDP
Samu kari