Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Tikitin Atiku/Okowa

Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Tikitin Atiku/Okowa

  • Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu gagarumin goyon baya a shiyyoyin kudu guda biyu
  • Jam'iyyun siyasa 40 ta bakin kungiyar CUPP sun yanke matsaya kan wanda zasu marawa baya a zaben Fabrairu
  • Sun bayyana Atiku/Okowa a matsayin tikitin da zai iya ceto ƙasar nan daga halin ƙaƙanikayi

Delta - Jam'iyyun siyasa 40 karkashin ƙungiyar gamayyar jam'iyyu (CUPP) reshen kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya sun yanke shawara game da zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jam'iyyun sun sha alwashin yin aiki tukuru domin nasarar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Yan takarar PDP.
Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Tikitin Atiku/Okowa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Kakakin gamayyar jam'iyyun, Prince Henry Eze, tare da shugaban Action Alliance (AA), Barista Ken Ikeh, da wasu shugabannin jam'iyun adawa 8 ne suka faɗi haka a Asaba, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan PDP

Manyan 'yan siyasan sun ce Atiku ne kaɗai zai iya ceto ƙasar nan daga halin da ta wayi gari a ciki ƙarƙashin mulkin jam'iyyar APC. Shugabannin suka ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Najeriya ta koma baya idan aka yi la'akari da zamanin PDP. Saboda haka muka yi duba a tsanake ta dawowar PDP ta hannun Atiku Abubakar da gwamna Ifeanyo Okowa na Delta."
"Zasu taka rawa mai kyau wajen sauya fasali, haɓaka da kuma haɗin kan ƙasar nan. Muna kira ga yan Najeriya su haɗa hannu damu wajen kafa daidaito, adalci da gaskiya a tikitin Atiku-Okowa, mu jingine batun addini."

Jam'iyyun sun ƙara da cewa burin Atiku da abokin takararsa Okowa wani linzami ne na samun abin da ƙasa ke fata saboda haka ya dace 'yan Najeriya su kaɗa musu kuri'nsu.

A cewarsu, tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta ɗauka tamkar cin mutunci ne ga ƙasar nan amma Atiku ya ɗauko abokan takararsa a 2019 da 2023 daga kudu maso gabas da kudu maso kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023

Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Legas

A wani labarin kuma Wasu tsageru sun farmaki ɗan takarar gwamnan jam'iyar PDP a jihar Legas, Abdul-Azeez Jandor

Lamarin dai ya haddasa musayar yawu tsakanin manyan jam'iyyu, APC mai mulki da kuma babbar jam'iyar adawa PDP.

Maharan waɗanda ake zaton yan daba ne sun bude wuta tare da lalata wasu daga cikin motocin Ayarin Jandor.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel