Kwankwaso Bai Da Kwarewar Mulkin Najeriya, Tsohon Sakataren NNPP

Kwankwaso Bai Da Kwarewar Mulkin Najeriya, Tsohon Sakataren NNPP

  • Dakta Babayo Liman, tsohon sakataren NNPP na shiyyar arewa maso gabas ya tona abinda ke wakana a jam'iyyar Kwankwaso
  • Liman ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano ba zai iya mulkin Najeriya ba saboda wasu dalilai da ya ambata
  • Ɗan siyasan ya ce ya sauya sheka zuwa PDP ne saboda ya goyi bayan Atiku Abubakar

Tsohon sakataren NNPP na shiyyar arewa maso gabas, Babayo Liman, ya ce jam'iyya mai kayan marmari da ɗan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, ba su da tsari da gogewar mulkin Najeriya.

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa Dakta Liman ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira da manema labarai a Jalingo, babban birnin Taraba ranar Lahadi.

Tsohon Sakataren NNPP, Babayo Liman.
Kwankwaso Bai Da Kwarewar Mulkin Najeriya, Tsohon Sakataren NNPP Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Ya ce ya yanke shawarin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ne saboda ya tallafa wa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: An Shiga Fargaba Yayin da Malamin Addini Ya Aika Gagarumin Gargadi Ga Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa

Dalilin da yasa Kwankwaso ba zai iya ba - Liman

Vanguard ta rahoto Liman na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"NNPP ba ta da kafaffen tsari da zai kai ga lashe zaɓe, ina kallon PDP a matsayin Direban da zata kai Najeriya tudun mun tsira daga kalubalen da ake fama da su. PDP da Atiku suna da tsarin cin zaɓe."
"Atiku na cikin gwamnatin Obasanjo da ake ganin ta samu nasarori da dama. Alal misali lokacin mulkin PDP, jihohi uku ke fama da matsalar tsaro amma yanzu ya karaɗe ko ina."
"Babu talauci kamar yanzu shiyasa na dawo inuwar Atiku. Kwankwaso ya nuna ƙarara cewa ba shi da kwarewar magance matsalolin 'yan Najeriya. Idan ba zai iya shawo kan rigimar ciki NNPP ba ta ya zai rike Najeriya."

"Ko a cikin shugabannin NNPP mu hudu ne muke aiki sauran duk bogi ne bamu taɓa ganinsu ba, ta ya irin wannan jam'iyyar zata iya nasara a zaɓe?" inji shi.

Kara karanta wannan

Akwai Babban Tanadi Da Na Yi Wa Yan Arewa Idan Na Zama Shugaban Kasa, Obi

Tsohon jigon NNPP ya ƙara da cewa kamar yadda al'adar siyasa ta tanada, ya zama tilas ya faɗa wa magoya bayansa matakin da ya ɗauka na sauya sheka da kuma inda zai koma.

Bugu da ƙari, Liman yace Kwankwaso ne ya ja hankalinsa zuwa NNPP sabida karɓuwarta a shiyyar amma tun da ya gaza sulhunta rigimar cikin gida, alama ce ta ba zai iya mulkin Najeriya ba.

APC ta sake babban rashi a Katsina

A wani labarin kuma Dan Majalisar Wakilan Tarayya Daga Katsina Ya Fice Daga Jam'iyar A APC

Ɗan majalisa mai wakiltar kananan hukumomi uku a majalisar wakilai, Hamza Dalhatu, ya fice daga APC zuwa jam'iyyar PDP.

Hamza, wanda ya rasa tikitin tazarce kan kujerarsa a APC, bai faɗi maƙasuɗin da ya sa ya fita daga jam'iyya mai mulki a ƙurarren lokaci da zaɓe ya ƙara matsowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel