Kanin Dan Takarar Gwamnan NNPP a Bauchi da Wasu Kusoshi Sun Koma PDP

Kanin Dan Takarar Gwamnan NNPP a Bauchi da Wasu Kusoshi Sun Koma PDP

  • Wata ɗaya da wasu kwanaki kafin zaben gwamnoni, ɗan takarar NNPP a Bauchi ya rasa manyan yan siyasa da makusantansa
  • Kanin mai neman zama gwamna a inuwar NNPP da wasu kusoshin siyasa sun koma PDP a taron Ganjuwa
  • Gwamna Muhammed na PDP ya nuna farin ciki da lamarin, inda yace alama ce ta mutane na son mulkinsa

Bauchi - Buhari Jika, kanin ɗan takarar gwamnan New Nigeria People Party a jihar Bauchi, Halliru Jika da wasu 'yan uwansa sun sauya sheƙa zuwa PDP mai mulki.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sun koma jam'iyyar PDP mai mulkin Bauchi domin su marawa kudirin neman tazarcen gwamna Bala Muhammed.

Sauya sheka a Bauchi.
Kanin Dan Takarar Gwamnan NNPP a Bauchi da Wasu Kusoshi Sun Koma PDP Hoto: punchng
Asali: UGC

Haka zalika, Ko-oditenan yakin neman zaben tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abubakar, watau Auwalu Ganjuwa, da shugaban ƙungiyar 'yan takara na jiha, Abbas Barde, sun koma PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023

Jiga-jigan siyasar sun sanar da sauya shekarsu a wurin gangamin kamfen Kauran Bauchi wanda ya gudana ranar Jumu'a a Kafin Madaki, ƙaramar hukumar Ganjuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka yanke komawa PDP?

Masu sauya shekar sun ce sun ɗauki wannan matakin ne bisa ganin tubalin ci gaba da gwamna Mohammed ya dora a Bauchi wanda ya kama hanyar sauya jihar.

Baya ga haka sun kuma zargi Sanatan Bauchi ta tsakiya, Haliru Jika, da ƙin agaza wa gwamna Muhammed ta hanyar jawo ayyukan raya ƙasa daga gwamnatin tarayya zuwa shiyyarsu.

Bugu da ƙari, jiga-jigan siyasan sun bayyana cewa tuni suka kammala shirin tara magoya baya domin cika burin tazarcen gwamna mai ci wanda haka ne kaɗai zai ba shi damar ci gaba da ayyukan da ya faro.

Da yake maraba da mutanen, Gwamna Muhammed ya yi na'am da sauya shekar inda ya kira matakin da suka ɗauka a matsayin wata alamar yarda da salon mulkinsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar Gwamna a Arewa Ya Janye, Ya Koma Bayan Jam'iyar PDP

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun kafin fara Ralin, gwamnan ya yi yawon duba ayyukan Tituna da suka haɗa gariruwa da ƙauyuƙa a sassan ƙaramar hukumar.

A wani labarin kuma Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023

Har yanzun dai babu alamun cewa za'a haɗa inuwa ɗaya tsakanin Atiku ɗa gwamnonin tawagar G-5 a PDP gabanin watan Fabrairu.

Gwamnonin su halarci Ralin PDP a jihar Enugu kuma sun sha alwashin.taimaka masu su ci zaɓe amma sun yu gum game da batun Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262