Gwamnan Jihar Da PDP Ke Mulki Zai Rufe Masallatai Da Coci-Coci A Jiharsa, Ya Bada Dalili

Gwamnan Jihar Da PDP Ke Mulki Zai Rufe Masallatai Da Coci-Coci A Jiharsa, Ya Bada Dalili

  • Za a rufe coci-coci, masallatai, dakunan taro, wuraren shakatawa da kasuwanci ire-iren su a Edo idan ba su daidaita sautin da ke fitowa daga cikinsu ba
  • Gwamnatin Jihar Edo ta fitar a wata sanarwa cewa ta bada wa'adin kwana 90 ga masu irin gine-ginen
  • Rahotanni sun bayyana cewa wa'adin zai kare ranar Juma'a, 31 ga Maris na 2023

Edo, Benin - Gwamnatin Jihar Edo ta bada gargadin karshe ga Cocina, Masallatai, wuraren taruka, da gidajen rawa da sauran wuraren shakatawa da ba su sanya na'urorin daidata sauti a gine-ginensu ba.

Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, gwamnatin Jihar tace wa'adin da aka bayar don takaita kara da za ta iya damun mutane zai kare ranar Juma'a, 31 ga watan Maris.

Godwin Obaseki
Gwamnan Jihar Da PDP Ke Mulki Zai Rufe Masallatai Da Coci-Coci A Jiharsa, Ya Bada Dalili. Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An zartar da matakin ne a wani taro tsakanin masu irin wannan gine-ginen dake da bukatar daidata sauti da kuma gwamnati.

Legit.ng ta tabbatar wata hukumar hadin gwiwa da aka kafa karkashin ma'aikatar tsare-tsare, cigaban birane da gunduma da kuma ma'aikatar muhalli ta tura kashedin karshe ga masu wuraren bauta da kasuwanci kan subi umarmin gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar kamar yadda ta fitar a wata sanarwa ta ce:

''An zartar da hukunci bayan taro tsakanin masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da kuma jami'an gwamnati kan bukatar sanya abun da zai takaita tashin kara, wanda aka yi ranar 31 ga Oktoba, 2022."

Mun tura sanarwa ga wanda abin ya shafa - Gwamnatin Edo

A wani rahoton, kwamishinan MPPHURD, Isoken Omo yace, sanarwar ta kunshi bayanai game da matsayar da aka cimma tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki don bin wannan dokar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

Da yake karin haske akan abin da ke kunshe a sanarwar, Isoken Omo ya ce:

''Masu irin wannan waurare suna da wa'adin kwana 90. An kuma makala wata takarda ta take kunshe da irin na'urorin da ya kamata ayi amfani da su, da kuma aikin ma'aikatar muhalli wajen karin bayani akan irin abin da ya kamata ayi amfani da shi.''.
''Anyi hakan dan takaita sakin kara barkatai zuwa yadda bazai dami mutane ba kamar yadda kunshe cikin dokar Muhalli ta kasa, mai lamba F.R.N part V 13-1308 17 - (2) da kuma dokikin tsara birane. Hakan kuma ya zama dole bayan da MPPHURD ta karfi dumbin korafi da kuma kararraki daga al'umma.''

Gwamnan Edo ya sallami kwamishinansa kan zargin baya aiki yadda ya kamata

Kun ji cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya sallami kwamishinansa na hanyoyi da gadoji, Injiniya Newton Okojie kan zargin cewa ba ya tabuka aikin azo-a-gani.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Kotu ta Baiwa DSS Muhimmin Umarni kan Tukur Mamu, Hadimin Gumi da Ake Zargi da Taimakon 'Yan Bindiga

Obaseki ya sanar da hakan ne cikin kunshin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai da wayar da kan al'umma na jihar, Chris Osa Nehikhare ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel