Shugabancin Kasa A 2023: IBB Ya Goyi Bayan Atiku? Dino Melaye Ya Aike Da Sako Ga Tsohon Shugaban Mulkin Soja

Shugabancin Kasa A 2023: IBB Ya Goyi Bayan Atiku? Dino Melaye Ya Aike Da Sako Ga Tsohon Shugaban Mulkin Soja

  • Tsohon dan majalisar tarayya na Kogi, Dino Melaye, yana ikirarin cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida yana goyon bayan Atiku Abubakar
  • Melaye ya bayyana godiyarsa ta tsohon shugaban mulkin sojan kuma ya bayyana labarin a shafin Facebook a ranar Juma'a, 27 ga watan Janairu
  • Tsohon sanatan ya ce Babangida ya bayyana matsayarsa kan ga kwamitin kamfen din Atikun ne ta hannun Mohammed Babangida a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu

Jihar Delta - A cewar Dino Melaye, tsohon sanata daga jihar Kogi wanda ya wakilici Kogi ta Yamma, Ibrahim Badamasi Babangida ya goyi bayan takarar shugaban kasa na Atiku Abubakar a zaben da ke tafe.

Ta shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 27 ga watan Janairu, Melaye, mai magana da yawun kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya ce an tabbatar da hakan a Jihar Delta ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, yayin kaddamar da wani aiki da Atiku ya yi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan Takarar Gwamna a Fitacciyar Jihar Arewa Ya Kwanta Dama Bayan Fama da Rashin Lafiya

Atiku da IBB
Shugabancin Kasa A 2023: IBB Ya Goyi Bayan Atiku? Dino Melaye Ya Aike Da Sako Ga Tsohon Shugaban Mulkin Soja. Hoto: (Photo: Dino Melaye)
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Melaye ya yi ikirarin cewa Babangida ya sanar da matsayinsa ta bakin dansa ne, Mohammed.

Wallafar na Melaye ta ce:

"Muna son mu gode wa iyalan tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida saboda goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasar Najeriya.
"Mohammed Babangida ne ya bayyana hakan a Jihar Delta a ranar Laraba yayin kaddamar da filin fina-finai da shakatawa na Maryam Babangida. Sanata Dino Melaye."

Asali: Legit.ng

Online view pixel