Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Atiku da PDP Ke Gudana Yau A Jihar Kebbi

Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Atiku da PDP Ke Gudana Yau A Jihar Kebbi

Kwamitin kamfen takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyya Peoples Democratic Party ta shiga jihar Kebbi, Arewa maso yammacin Najeriya a yau Asabar, 28 ga watan Junairu, 2023.

Dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar; abokin tafiyarsa, Ifeanyi Okowa; shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigai sun dira Kebbi.

"Mun tabbata PDP ta cinye Kebbi, Mun sani, mun iya, mun yadda yadda zamu yi" Atiku Abubakar

Jawabin Atiku

"Mun tabbata PDP ta cinye Kebbi. Ni kuma a matsayina na dan takarar shugaban kasa, idan kuka zabeni zan tabbatar muku da abubuwa guda uku
- rashin tsaro dake fama a Kebbi da sauran jihohi arewa maso yamma zamu magance.. da yardan Allah zamu dawo da zaman lafiya.
- Dam din jihar Kebbi dake bawa manoma ruwa har da Sokoto, muna tabbatar muku zamu yashe Dam din don dawo da ruwa
- Na dauki alkawari zan bude boda. Gaba daya cikin yan takara babu wanda ya san harkar Boda kama na. Zamu bude boda domin kasuwanci.
"Mun sani, mun iya, mun yadda yadda zamu yi."
"Ina jajanta muku game da kashe-kashe da akayi da kuma ambaliyar ruwa. Allah ya kiyaye."

APC ta yi muku alkawarin canji amma sai dai aka ga canje-canje

Shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, a jawabinda ya yi kira ga al'ummar Kebbi kada su sake zaben jam'iyyar APC.

Ayu yace APC ta yiwa yan Najeriya alkawarin canji amma sai dai suka ga canje-canje.

"APC sun gama mana kamfe, saboda basu son abinda suke ba. Al'ummar Kebbi kun san wanda zaku zaba. Najeriya sai Atiku."

Iyorchia
Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Atiku da PDP Ke Gudana Yau A Jihar Kebbi
Asali: UGC

Kashim Shettima Shine Shugaban Yan Boko Haram, Hajia Naja'atu

Hajia Naja'atu Usman ta bayyana cewa dan takaran mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, shine shugaban yan ta'addan Boko Haram.

Ta bayyana cewa Allah ya kiyaye shugaban yan ta'adda ya zama mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Ta ce dalilin da yas ata fadi hakan shine lokacin da Kabiru Sokoto, dan Boko Haram ya kai hari Bam cocin Katolika a jihar Neja, gidan Kashim Shettima ya boye.

Mun dira jihar Kebbi, zamu kwace Najeriya: Atiku

Jama'a sun yi cincirindo a wajen taro

Taron kamfe ya kankama a Filin Sukuwa dake birnin Kebbi.

Farfajiyar ta cika ta banbatse da mabiya jam'iyyar PDP.

Online view pixel