Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta Na Jihar Ebonyi Kan Cin Amana

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta Na Jihar Ebonyi Kan Cin Amana

  • Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP ta ƙara shiga cikin hatsaniya bayan rigimar da ake fama da tsagin Wike
  • Kwamitin ayyuka na kasa ya snaar da dakatar da shugaban PDP na jihar Ebonyi Okoroafor biza zargin da ake masa
  • PDP ta kuma sanar da naɗa kwamitin rikon kwarya a jihar Ekiti bayan ta kori zababbun shugabanni a makon da ya shige

Ebonyi - Kwamitin ayyuka na jam'iyyar PDP ta ƙasa ya dakatar da shugaban jam'iyya na jihar Ebonyi, Okorie Tochukwu Okoroafor, bisa zargin cin amana.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa bayan haka, PDP ta sanar da kafa kwamitin rikon kwarya a reshen jihar Ekiti karkashin jagorancin Sadiq Obanoyen.

Jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shugabanta Na Jihar Ebonyi Kan Cin Amana Hoto: thenation
Asali: UGC

Mai magana da yawun PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a 27 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Ganduje Ya Ɗage Ziyarar da Buhari Zai Kawo Kano Kan Abu 1 da Ya shafi Canjin Kuɗi

Yace a halin yanzu shugaban PDP na Ebonyi da aka dakatar zai gurfana a gaban kwamitin ladabtarea domin ɗaukar mataki na gaba a kansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ologunagba ya yi bayanin cewa an cimma matsayar dakatar da Mista Okoroafor a wurin taron gaggawa da PDP-NWC ya gudanar ranar Jumu'a.

Sanarwan ta ƙara da cewa ana zargin Okoroafor ya saɓa wa tanadin sashi na 58 (1) da ke ƙunshe a kundin mulkin PDP wanda aka yi wa garambawul a 2017, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

PDP ta naɗa kwamitin rikon kwarya a Ekiti

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa idan baku manta ba a ranar 20 ga watan Janairu, Jam'iyyar PDP ta kori shugabanninta na reshen jihar Ekiti kana ta naɗa Obanoyen a matsayin shugaban riko.

Mambobin kwamitin rikon kwaryan da PDP ta naɗa sun ƙunshi, Ojoade Fajana, Adijat Eniola Balogun, Oladimeji Joshua Ayodele, Boboye Adekunle, Lawal Idayat Tosin, Waliu Olawole Oladipupo da Erelu Toyin Olumilua Mark.

Kara karanta wannan

Ta Kacame: APC Ta Fatattaki Wani Ministan Buhari Daga Jam'iyya? Gaskiya Ta Bayyana

Sauran kuma su ne, Alade Beatrice Modupe, Temitope Amerijoye, Akogun Bunmi Ogunleye, Olugbenga Adewole, Ajibola Samuel da kuma Dosu Babatunde wanda aka naɗa a matsayin Sakatare.

Atiku Na Shiga Rigunan Ayyukan Mu Domin Samun Nasara a Oyo, Makinde

A wani labarin kuma Gwamnan Oyo ya maida martani mai zafi ga tsohon Ministan makamashi game da Atiku

Gwamna Seyi Makinde, matasho daga cikin gwamnonin tawagar G-5 ya ce Atiku ne ke shiga rigarsa don ya ci zabe a jihar Oyo.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ta jihar tana tunkaho ne da ayyukan gwamnatinsa wajen neman samun nasara a zaɓuka masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel