Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Legas

Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Legas

  • Yan daba sun kai hari kan ayarin ɗan takarar gwamnan jihar Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran watau Jandor
  • Lamarin dai ya haddasa musayar yawu tsakanin manyan jam'iyyu, APC mai mulki da kuma babbar jam'iyar adawa PDP
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Legas yace babu wanda ya rasa ransa a lamarin

Wasu mutane sun kai hari kan tawagar ɗan takarar gwamnan jihar Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran wanda aka fi sani da Jandor a yankin Coker, Aguda da ke ƙaramar hukumar Surulere.

Maharan waɗanda ake zaton yan daba ne sun bude wuta tare da lalata wasu daga cikin motocin Ayarin Jandor yayin harin na ranar Jumu'a 27 ga watan Janairu, 2023.

Jandor.
Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Legas Hoto: Abdul-Azeez Adediran
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin wannan harin, 'yan daban sun tafka ɓarna kuma sun jikkata akalla mutane uku suna Asibiti kwance.

Kara karanta wannan

2023: Ta Ƙarewa Kwankwaso, Wasu Manyan Jiga-Jigan NNPP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Jandor tare da wasu mambobin PDP sun halarci taro da 'yan kasuwa da wasu ƙungiyoyi a yankin ƙaramar hukumar Surulere, jim kaɗam bayan haka ne aka kai masu hari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a halin yanzu jam'iyyun PDP da APC mai mulki sun zargi junansu da ɗaukar nauyin harin.

APC ya dora laifi kan tawagar Jandor

A wata sanarwa da kakakin APC na Legas, Seye Oladejo, ya fitar kuma jaridar Vanguard ta gani, ya ce:

"An ja hankalin mu kan wani harin ta'addanci da aka kaiwa mutanen da ba ruwansu, ɗan takarar gwamnan PDP da ya fi shahara da Jandor ake zargi da ɗaukar nauyi yayin kamfe dinsa a Surulere."
"Lamarin ya jikkata mutane da dama kuma mutum uku suka mutu, muna Allah wadai da lamarin da ke taɓa lafiyar talakawa da sunan Kamfe."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023

PDP ta maida martani

Haka nan kakakin PDP a Legas, Hakeem Amode, ya zargi jam'iyyar APC da ɗaukar nauyin 'yan daba su farmaki ayarin ɗan takarar.

"APC ta turo yan daba su ta da yamutsi a ƙaramar hukumar Surulere gabanin ziyarar da ɗan takarar gwamnan PDP ya kai gundumar ranakun Alhamis da Jumu'a."
"Maharan sun je fadar Baale na Ojuoluwa suka ja masa kunne kar ya sake ya bari a zo wajensa, suka kulle wurin. Haka nan yan daban ɗauke da muggan makamai da APC ta turo sun lalata runfuna da kujerun wurin taron."

"Sun lalata kayan da aka shirya a Iponri Housing Estate kuma da yawan mambobin mu dake tsara wurin sun samu raunuka," inji kakakin PDP.

Da yake tabbatar da lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce babu wanda ya mutu a lamarin amma akwai wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

2023: Rigima Ta Kara Ɓarkewa a PDP Bayan Su Wike, An Dakatar da Shugaban Jam'iyya na Wata Jiha

A wani labarin kuma Kotu Ta Tunbuke Sanatan Da Ya Fice Daga PDP, Ta Nemi INEC ta shirya Zaben maye gurbi

Babbar Kotun tarayya a Abuja ta tsige Sanata mai wakiltar mazaɓar Arewa maso gabashin jihar Akwa Ibom, Albert Akpan

Kotu ta tunbuke shi daga kujerar Sanata ne sabida sauya shekar da ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa Young Progressives Party (YPP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel