Kotu Ta Tunbuke Sanatan Da Ya Fice Daga PDP, Ta Nemi a Sauya Zabe

Kotu Ta Tunbuke Sanatan Da Ya Fice Daga PDP, Ta Nemi a Sauya Zabe

  • Babbar Kotun tarayya a Abuja ta tsige Sanata mai wakiltar mazaɓar Arewa maso gabashin jihar Akwa Ibom, Albert Akpan
  • Kotun ta dauki wannan mataki ne bisa hujjar Sanatan ya fita daga PDP babu wani dalili bayan ita ta ɗauki nauyinsa ya ci zaɓe
  • Sanata Akpan, ya sauya sheka daga PDP zuwa YPP inda ya samu tikitin takarar gwamna a zaɓe mai zuwa

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta tsige Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso gabas, Albert Akpan, sakamakon ficewar da ya yi daga jam'iyyar PDP.

Kotun ta ayyana kujerarsa da wacce babu kowa kana ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shirya zaben cike gurbi a mazabar Sanatan cikin kwanaki 14.

Sanata Akpan.
Kotu Ta Tunbuke Sanatan Da Ya Fice Daga PDP, Ta Nemi a Sauya Zabe Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Jaridar Prrmium Times ta ruwaito cewa wannan hukuncin ba shi da alaƙa da laifin da Mista Akpan ya aikata na cin hanci wanda Kotu ta tura shi gidan yari kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Na Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Cewar Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow

Kotu ta tunbuke shi daga kujerar Sanata ne sabida sauya shekar da ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa Young Progressives Party (YPP).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take yanke hukunci kan karar da PDP ta shigar, Mai shari'a Faɗima Aminu, ta yanke cewa Mista Akpan bai cancanci cigaba da zama a muƙamin ba bayan ya fita daga jam'iyyar data kai shi ga nasara.

Alkalin ta umarci Akpan da ya daina ayyana kansa a matsayin Sanata kuma ta umarce shi da ya baiwa jam'iyyar PDP mai ƙara miliyan N5m kan sauya shekar da ya yi zuwa YPP.

Mai shari'a Faɗima ta kara da cewa Akpan, sanata tsawon zango biyu, ya gaza kare kansa kan dalilin da ya tilasta masa sauya sheka daga PDP.

Sakamakon rashin gamsasshen jawabi, Alkalin ta ce sauya shekar da ya yi ta saba wa sashi na 68(1)(g) na kundin mulkin Najeriya wanda ya tanadi cewa dole ya bar kujerarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hadari Kusa Da Kubwa Abuja

Kanin Dan Takarar Gwamnan NNPP a Bauchi da Wasu Kusoshi Sun Koma PDP

A wani labarin kuma Wata ɗaya da wasu kwanaki kafin zaben gwamnoni, ɗan takarar NNPP a Bauchi ya rasa manyan yan siyasa da makusantansa

Rahotanni sun bayyana kanin ɗan takarar gwamnan NNPP a Bauchi, tare da wasu yan uwansa sun sauya sheƙa zuwa PDP domin mara wa Kauran Bauchi baya.

Jiga-jigan siyasar sun sanar da sauya shekarsu a wurin gangamin kamfen neman tazarce wanda ya gudana ranar Jumu'a a Kafin Madaki, ƙaramar hukumar Ganjuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel