Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar APC karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta karbi sabbin tuba bayan tsohon Minista da kuma Sanatan PDP daga jihar Enugu sun koma jam'iyyar.
Majalisar dokokin jihar Rivers ta bayyana manufarta na tsige gwamna Fubara duba da wasu abubuwan da suka ce sun saba da abin da suke tsammani game da shi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan hanyoyin da kundin tsarin mulki ya shimfida na tsige zababbun shugabanni daga karagar mulki, ciki har da shi kansa.
Mambobi 6 na majalisar dokokin jihar Enugu sun sauya sheka daga Labour Party da aka zaɓe su karkashinta, sun koma jam'iyyar PDP mai mulkin jihar kan wani daili.
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya watsar da kashin Atiku Abubakar inda ya marawa Shugaba Tinubu baya da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sha alwashin hukunta 'ya'yanta da suka ci dunduniyarta a lokacin babban zaben da aka gudanar a shekarar 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake birkita 'yan siyasa yayin da ya yi ganawa ta musamman da shugabannin jam'iyyar APC da kuma na 'yan adawa.
Deji Adeyanju ya yi magana kan motsin da Nasir El-Rufa'i da Peter Obi suke yi kan siyasar kasar nan. Deji ya ce Shugaba Bola Tinubu za su yi wa aiki a 2027.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya ce ba zai yi gigin tarar faɗa da shugaban kasa ba saboda shi ne juya akalar kuɗaɗen shigar jihar da yake mulki.
Jam'iyyar PDP
Samu kari