Jam'iyyar APC Ta Bankado Sabuwar Makarkashiyar da Gwamnan PDP Yake Kullawa

Jam'iyyar APC Ta Bankado Sabuwar Makarkashiyar da Gwamnan PDP Yake Kullawa

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers, ta zargi Gwamna Siminalayi Fubara da kitsa yadda za a haramta majalisar dokokin jihar
  • Jam'iyyar adawar ta bayyana cewa gwamnan yana ƙoƙarin samo wani umurnin kotu wanda zai haramta majalisar, domin ya naɗa shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar
  • Sai dai, gwamnatin jihar ta musanta wannan zargin wanda ta bayyana a matsayin mara tushe ballantana makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ribas - Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta zargi Gwamna Siminalayi Fubara da ƙoƙarin haramta majalisar dokokin jihar.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa gwamnan yana ƙoƙarin samo wani umurnin kotu wanda zai bayyana majalisar dokokin jihar a matsayin haramtacciya, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana muhimmin shirin da take yi wa marayu da nakasassu

APC ta zargi Gwamna Fubars
Alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Fubara da jam'iyyar APC Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

APC v Fubara: An fallasa shirin Gwamnan Ribas

Shugaban riƙo na jam'iyyar APC a jihar, Cif Tony Okocha, shi ne ya yi wannan zargin yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Fatakwal, a ranar Alhamis, 4 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha ya bayyana cewa gwamnan yana so ya yi amfani da umurnin kotun wajen naɗa shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar guda 23.

Shugaban na jam'iyyar APC ya ce jam'iyyar a matsayinta nta babbar jam'iyyar adawa a jihar, za ta yi duk abin da ya dace bisa doka domin ganin wannan shirin bai tabbata ba.

Me gwamnatin jihar ta ce kan zargin?

Sai dai, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Warisenibo Joe Johnson, ya bayyana zarge-zargen na APC a matsayin marasa tushe ballantana makama, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Johnson ya ce APC ta firgita ne saboda yadda ta ga al'ummar jihar na nuna tsantsar ƙauna ga gwamnan.

Kara karanta wannan

Takaddamar El-Rufai da Uba Sani: Jam'iyyar APC ta fadi wanda take goyon baya

Gwamna Fubara ya gargaɗi masu sukarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya gargadi masu sukarsa da kada su kuskura su kai shi bango.

Gwamnan ya bayyana cewa ya yanke shawarar fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ne kawai saboda yana mutunta shugaban ƙasa, mai girma Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel