APC Ta Sake Batsewa Bayan Jiga-jigan PDP 8 Sun Watsar da Jamiyyarsu Ana Daf da Zaɓe

APC Ta Sake Batsewa Bayan Jiga-jigan PDP 8 Sun Watsar da Jamiyyarsu Ana Daf da Zaɓe

  • An daf da gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, wasu tsofaffin shugabannin kananan hukumomi sun koma APC
  • Aƙalla tsofaffin ciyamomi takwas ne suka sauya shekar zuwa jam'iyya mai mulkin Najeriya ta APC a jihar
  • Sanata Adams Oshiomole shi ya karbi sababbin tuban a gidansa da ke birnin Benin a jiya Litinin 1 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Tsofaffin shugabannin kananan hukumomi takwas ne suka watsar da jamiyyarsu ta PDP a jihar Edo.

Jiga-jigan PDP sun sauya sheka ne zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

PDP ta sake samun naƙasu bayan jiga-jiganta 8 sun koma APC
Tsofaffin ciyamomin kananan hukumomi 8 ne 'yan PDP suka koma APC a Edo. Hoto: Umar Ganduje, Umar Damagun.
Asali: Facebook

Jerin wadanda suka koma APC daga PDP

Wadanda suka sauya sheka sun hada da John Akhigbe da Dakta Josie Ogedegbe da Frank Ilaboya da Andrew Osigwe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Napoleon Agbama da Uhunmwonde da Scott Ogbemudia da Austin Okoibhole da Ruth Osahor.

Sababbin tuban sun samu tarba daga Sanata Adams Oshiomole a jiya Litinin 1 ga watan Maris a gidansa da ke Benin City.

Sanata Oshiomole ya yi maraba da su inda ya ba su tabbacin daukarsu tamkar wadanda suka dade a jami'yyar.

Tarbar da suka samu daga Sanata Oshiomole

"A madadin shugaban APC a Edo da gwamna mai jiran gado, Monday Okpebholo da mataimakinsa, ina maraba da ku."
"Wadannan mutane ne Ubangiji ya yi amfani da ni na kai su ACN yanzu kuma sun dawo APC."
"Sun ba da gudunmawa sosai a gwamnati, wasu a cikinsu sun rike shugabannin kananan hukumomi a gwamnatina."

Kara karanta wannan

Rikicin Jihar Plateau: Fulani na zargin sojojin Najeriya da yi masu bakin aika-aikata

- Adams Oshiomole

Oshiomole ya ce a kowane gida ana samun baraka, amma abin murna yanzu shi ne waɗannan sun gane gaskiya sun dawo gida, cewar Daily Post.

Jiga-jigan PDP sun koma APC a Enugu

Kun ji cewa wasu jiga-jigai a jam'iyyar PDP sun watsar da ita tare da komawa jami'yyar APC a jihar Enugu.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar akwai tsohon sanata, Chuka Utazi da tsohuwar ministar Sufuri da kuma sauran jiga-jigan jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel