Daga Karshe Wike Ya Bayyana Inda Aka Kwana Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

Daga Karshe Wike Ya Bayyana Inda Aka Kwana Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi ƙarin bayani kan rikicin da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara
  • Wike ya ce ba ya cikin inuwa ɗaya a siyasance da Gwamna Fubara kuma ba shi da hannu a rikicinsa da ƴan majalisar dokokin jihar
  • Ministan ya kuma bayyana cewa yanzu ba shi da kyakykyawar alaƙa da tsohon gwamnan jihar, Peter Odili

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce yanzu shi da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ba su a inuwa ɗaya a siyasance duk da suna cikin jam’iyyar PDP.

Wike ya ce ba shi da hannu kan barazanar tsige Gwamna Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar Ribas ke yi.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

Wike ya yi magana kan rikicinsa da Fubara
Wike ya ce ya raba gari da Gwamna Fubara Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Ministan ya ce bai damu da rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar ba, inji rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya haɗa Wike da Fubara rigima?

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya dage cewa ya mayar da hankali ne kan aikin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi.

A kalamansa:

"Na yanke shawarar cewa ba zan damu kaina da batun siyasa ba sai aikin da Shugaba Tinubu ya bani. Ban je gida hutun Easter ba. Meyasa kuke tunanin ina da ta cewa kan abin da ke faruwa a majalisar dokokin?"

Sai dai, ministan ya ce ba zai bar ginin siyasar da ya yi a jihar Ribas ba saboda yana da aikin yi a Abuja.

Wike na rigima da Peter Odili

Gidan talabijin na Channels ya rahoto cewa Wike ya ce yanzu ba shi da kyakykyawar alaƙa da tsohon gwamna, Peter Odili, saboda "akwai bambance-bambancen siyasa".

Kara karanta wannan

Adejanyu ya lissafo ministocin Tinubu 2 da ya kamata ya kora, ya zayyano dalilai

Wike a baya ya sha bayyana Odili a matsayin ubangidansa kuma jagoransa na siyasa.

A cewarsa:

"Kamar yadda yake a yau, a siyasance, ba mu da kyakkyawar dangantaka. Ba mu aiki tare."

Gwamna Fubara ya biya kuɗin maniyyata

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ɗauki nauyin biyan cikin kuɗin hajji ga maniyyata a jihar.

Gwamnan ya biya cikon kuɗin kujerun ne bayan hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi ƙarin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel