'Yan Majalisa 6 Sun Yanke Shawara, Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP Kan Matsala 1

'Yan Majalisa 6 Sun Yanke Shawara, Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP Kan Matsala 1

  • Yayin da Labour Party ke fama da rikicin cikin gida, mambobi 6 na majalisar dokokin jihar Enugu sun sauya sheƙa zuwa PDP
  • Sun bayyana cewa sun gaji da matsalolin da suka dabaibaye LP a matakin ƙasa da jihohi, bisa haka suka koma PDP domin yi wa al'umma hidima
  • A baya-bayan nan LP ta sha fama da rigima kan shugabancin jam'iyya na ƙasa musamman tsakanin Julius Abure da Lamidi Apapa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - ‘Yan majalisar dokokin jihar Enugu su shida da aka zaba a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP) sun sanar da sauya sheka a hukumance.

Ƴan majalisar sun sauya sheƙa daga LP zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar Enugu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar mutum 313 da ake zargi da aikata ta'addanci

Jam'iyyar PDP.
Labour Party ta rasa ƴan majalisa 6 a jihar Enugu Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Mambobin majalisar sun sanar da sauya shekar su a hukumance ne a harabar majalisar a zamanta na ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan majalisar suka bar LP?

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda “rarrabuwar kawuna, da rikicin da ya barke a Labour Party a matakin kasa da rassan jihohi."

“Abin takaici, jam’iyyar ta rikiɗe zuwa wani yanayi na rashin jituwa tsakanin mambobi tare da darewa zuwa ɓangarori daban-daban da suka fara fadace-fadacen shari’a."
"A baya LP jam'iyya ce mai ƙunshe da manufar kawo ci gaba, amma abin nadama a yanzu ta zama fagen rigingimun cikin gida, wanda ya dakushe yunkurinta na cika burin al'umma," in ji su.

Sun bayar da misali da rikicin shugabanci tsakanin bangarorin Julius Abure da Lamidi Apapa da badaƙalar da ma'ajiyar ƙasa ta bankaɗo a matsayin wasu daga cikin rigingimun da suka dabaibaye LP.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Abubuwan sani 5 dangane da jana'izar da za a yi wa jami'an tsaron

Sun yi fatan cewa PDP za ta ba su damar da za su ci gaba da yi wa al’ummarsu hidima, kana suka gode wa shugabannin LP bisa goyon bayan da suka ba su, Daily Trust ta ruwaito.

Jerin ƴan majalisar da suka koma PDP

Wadanda suka sauya shekar sun hada da mai ladabtarwa na majalisa kuma mai wakiltar Igboeze ta Arewa I, Ejike Eze da jagoran majalisa kuma mamba mai wakiltar Enugu ta Arewa, Johnson Ugwu.

Sauran su ne mai wakiltar Enugu ta Kudu, Princess Ugwu, mai wakiltar Nsukka ta Yamma, Pius Ezeugwu, mai wakiltar Igbo-Etiti ta Gabas, Amuka Williams, mai wakiltar Oji River, Osita Eze.

An naɗa sabon shugaban NNPP

A wani rahoton kuma Ajuji Ahmed ya zama sabon shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa.

Jam’iyyar ta sanar da naɗinsa ne a wata sanarwa ranar Talata, 26 ga watan Maris, ta hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Yakubu Shendam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel