Zaben 2027: An Bayyana Abin da El-Rufa'i da Peter Obi Za Su Yi Wa Tinubu

Zaben 2027: An Bayyana Abin da El-Rufa'i da Peter Obi Za Su Yi Wa Tinubu

  • Wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju ya bayyana ra'ayinsa game da yanayin siyasar Najeriya
  • Adeyanju ya tabbatar da cewa jiga-jigai irin su Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) da Nasir El-Rufa'i na jam’iyyar APC, ƴan ɗauke hankali ne kawai
  • Deji ya bayyana su a matsayin "ƴan aiki" na siyasa, yana mai nuni da cewa suna ƙoƙarin kawo cikas domin samar da adawa mai ƙarfi a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, kuma kuma ɗan fafutuka, Deji Adeyanju ya ce Peter Obi, na jam’iyyar Labour Party (LP) da Nasir El-Rufa'i na jam'iyyar APC, ƴan ɗauke hankali ne kawai.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, 22 ga watan Maris, Adeyanju ya bayyana mutanen biyu a matsayin “ƴan aiki” na siyasa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

El-Rufa'i, Peter Obi da Bola Tinubu
Adeyanju ya ce Peter Obi da El-Rufa'i za su yi wa Tinubu aiki a 2027 Hoto: Mr Peter Obi/Bola Ahmed Tinubu/Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Ya yi iƙirarin cewa abubuwan da suke yi ba komai ba ne face ɗauke hankali, da ƙoƙarin ɓata yunƙurin samar da adawa mai ƙarfi a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanan nan Obi ya ziyarci wasu manyan masallatai biyu a jihohin Nasarawa da Neja, inda ya saurari tafsir tare da yin buɗa baki da al'ummar musulmi.

El-Rufa'i da Obi na shiri kan 2027

Hakazalika, El-Rufai ya yi ziyarce-ziyarce, inda ya ziyarci shugaban jam’iyyar SDP, Femi Fani Kayode (APC), da Sanata Abdul Ningi, Sanatan PDP da aka dakatar.

An yi hasashen cewa abin da ƴan siyasan biyu ke yi, suna yi ne domin fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Adayanju, a cikin martanin da ya yi game da batun, ya bayyana cewa:

"Obi da El-Rufa'i masu ɗauke hankali ne a siyasa. Dukkansu za su yi wa Tinubu aiki kamar yadda suka yi a zaɓen da ya gabata, da yin zagon ƙasa kan samar da adawa mai ƙarfi. Ƴan aiki ne."

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

El-Rufa'i ya ziyarci Abdul Ningi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i, ya kai ziyara ga Sanata Abdul Ningi.

Ziyarar Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, na daga cikin ziyarce-ziyarcen manyan ƴan siyasa da El-Rufa'i ke ci gaba da yi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel