Ganduje Ya Karbi Sabbin Tuba Bayan Tsohon Sanata da Ministan PDP Sun Koma APC

Ganduje Ya Karbi Sabbin Tuba Bayan Tsohon Sanata da Ministan PDP Sun Koma APC

  • Jam'iyyar APC ta sake samun ƙarfi bayan tsohon minista da sanata sun sauya sheka zuwa jam'iyyar
  • Sanata Chuka Utazi da tsohuwar Ministar Sufuri, Fidelia Njeze duk sun watsar da jam'iyyarsu tare da dawo wa APC
  • Har ila yau, dan takarar gwamnan Enugu a zaben 2023, Dakta Dave Nnamani shi ma ya watsar da jam'iyyarsa ta LP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Jiga-jigan jam'iyyar PDP da LP a jihar Enugu sun sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai mulki.

Tsohon Sanata Chuka Utazi da tsohuwar Minista, Fidelia Njeze da suka koma LP a zaben 2023 duk sun sauya sheka zuwa APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwashe bayan tsohon shugaban PDP da jiga-jiganta, sun watsar da Atiku

APC ta samu karuwa bayan Ganduje ya karbi sabbin tuba daga wasu jam'iyyu
APC karkashin jagorancin Umar Ganduje ta karbi tsohon Sanata da Minista bayan sun sauya sheka. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Wadanda suka watsar da jam'iyyunsu zuwa APC

Har ila yau, dan takarar gwamnan jihar Enugu a jami'yyar LP, Dakta Dave Nnamani shi ma ya watsar da jami'yyarsa inda ya koma APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da 'yan takarar sanata a jam'iyyun APGA da ADC da magoya bayansu sun karawa jam'iyyar APC karfi.

Sabbin tuban sun samu tarba daga shugaban APC a jihar, Ugochukwu Agballa da kuma Ministan kimiyya da fasaha, Mista Uche Nnaji, cewar Daily Post.

Alkawuran da APC ta yiwa sauran 'yan adawa

Shugabannin jam'iyyar sun bayyana himmatuwarsu wurin karbar duk wadanda ke shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar.

Sun kuma ba da tabbacin gyara duk wata matsala a jam'iyyar kama daga wadanda aka dakatar ko kora sakamakon sabani da aka samu.

Daga bisani jam'iyyar ta taya Shugaba Bola Tinubu murnar cika shekaru 72 a duniya inda ta masa fatan alheri.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa 6 sun yanke shawara, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP kan matsala 1

Mambobin Majalisar Enugu 6 sun koma PDP

A wani labarin, mambobin Majalisar jihar Enugu da ke jam'iyyar LP sun watsar da ita tare sauya sheka zuwa PDP.

Mambobin majalisar sun sanar da sauya shekar su a hukumance ne a harabar majalisar a zamanta na ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne ganin yadda ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna kan rikicin shugabnci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel