"Rashin Ɗa'a": An Fara Zama Kan Batun Tsige Mataimakin Gwamna, Bayanai Sun Fito

"Rashin Ɗa'a": An Fara Zama Kan Batun Tsige Mataimakin Gwamna, Bayanai Sun Fito

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, na tsaka mai wuya yayin da kwamitin da aka kafa ya fara zama ranar Laraba
  • Tun farko babban alkalin jihar Edo ya kafa kwamitim mutum 7 da zai binciki zargin da ake yi wa Shaibu wanda ya jawo majalisa ke shirin tsige shi
  • Majalisar dokokin Edo ta fara shirin tunɓuƙe Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna kan zargin rashin ɗa'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Kwamitin mutum bakwai da aka kafa domin binciken zargin rashin da’a da ake yiwa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya fara zama a Benin.

Babban alkalin jihar Edo, Daniel Okungbowa, ne ya kafa kwamitin a karkashin jagorancin, S. A. Omonuwa, tsohon akalin da ya yi ritaya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC zai ɗauki sababbin ma'aikata sama da 5,000 a jiharsa, ya faɗi dalili

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
An fara zaman bincike kan zargin da ake wa Shaibu a Edo Hoto: Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Wannan kwamitin ya fara zama ne biyo bayan shirin majalisar dokokin jihar na tsige mataimakin gwamnan kan zargin rashin ɗa'a da ladabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake shirin tsige Shaibu?

Idan ba ku manta ba, an jima ana zaman doya da manja tsakanin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da mataimakinsa, Kwamared Philip Shaibu.

A zaman farko na kwamitin a ranar Laraba, majalisar dokoki ta samu wakilcin Joe Ohiafi, mataimakin magatakarda na sashin shari'a.

Shaibu ya samu wakilcin Oladoyin Awoyale, Farfesa kuma babban lauya a Najeriya (SAN), kamar yadda Leadership ta rahoto.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun George Odidi, sakataren gudanarwa na kwamitin, a makon da ya gabata, ta ce:

"Muna sanar da cewa bayan kaddamar da wannan kwamiti kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, zai fara zama a ɗakin taron alkalai da ke sabon ginin babbar kotun jiha a Benin.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta ɗauki mataki kan ɗan Kwankwaso da mutum 3 da Gwamna Yusuf ya naɗa

"Kwamitin zai fara wannan zama ne ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, 2024 daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa abin da ya sawwaƙa. Muna fatan kowane ɓangare ko lauyoyinsu za su halarci zaman a wannan rana."

Wannan dai na zuwa ne bayan kammala zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, wanda Shaibu ya jaddada cewa shi ne halastaccen ɗan takara.

Shaibu ya yi rashin nasara a kotu

A.wani rahoton kuma Mataimakin gwamnan jihar Edo ya yi rashin nasara a babbar kotun tarayya yayin da yake kokarin hana majalisar dokoki tsige shi.

Alkalin kotun, mai shari'a James Omotoso, ya ƙi aminta da ko ɗaya daga cikin buƙatun Kwamared Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel