APC Ta Yi Kamu Bayan Jiga-Jigan PDP Sun Dawo Tafiyar Ganduje, Tsohon Gwamna na Kan Hanya

APC Ta Yi Kamu Bayan Jiga-Jigan PDP Sun Dawo Tafiyar Ganduje, Tsohon Gwamna na Kan Hanya

  • Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Abia bayan tsofaffin kwamishinoni a jihar sun watsar da tafiyar jam'iyyar PDP
  • Jiga-jigan dai sun riƙe muƙamai a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Okezie Ikpeazu na jam'iyyar PDP
  • Sauya sheƙar ta su ta sanya an fara raɗe-raɗin cewa Ikpeazu ya fara shirin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Umuahia, jihar Abia - Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Abia bayan wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun dawo cikinta.

Anthony Agbazuere, shugaban ma’aikatan fadar tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin da ta gabata sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

Jiga-jigan PDP sun koma APC a Abia
Ana rade-radin Okezie Ikpeazu zai koma APC Hoto: @OfficialAPCNg, @OkezieIkpeazu
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta kawo rahoto a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, cewa masu sauya sheƙar sun koma jam'iyyar APC ne bayan sun fice daga jam’iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai da dabaru, Barista Eze Chikamnayo daga Umunneochi da tsohon kwamishina a hukumar NDDC, Cif Chimezie Okoronkwo.

Sun dai sauya sheƙar ne a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Umunneochi gabanin taron jiga-jigan jam’iyyar APC na shiyyar a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, rahoton da jaridar Daily Post ya tabbatar.

Ikpeazu zai iya komawa APC

Duk da cewa sansanin tsohon gwamnan ya yi shiru kan yadda ƴaƴan jam’iyyar suka fice daga jam’iyyar PDP, wasu na ganin hakan na iya zama wani ɓangare na yunƙurin share fage domin Ikpeazu ya koma APC.

Kara karanta wannan

INEC ta jero sunayen jam'iyyun siyasa 19 da za su fafata a zaben gwamnan jihar Ondo

Da yake tarbarsu zuwa cikin jam'iyyar, sakataren walwala na ƙasa na jam’iyyar APC, Donatus Nwankpa, ya bayyana cewa:

"Ƙullin siyasa ne kawai. Yana daga cikin juyin juya hali na siyasa. Shigowarsu jam'iyyar APC zai ƙara mata ƙarfi.
"Sun bada tabbacin cewa za su jawo sauran mabiyansu zuwa cikin jam'iyyar tare da kawo ci gaba.
"Sun bayyana cewa sun fahimci lokaci ya yi da za su dawo cikin jam'iyya mai mulki a ƙasa domin a dama da su.
"Za su kawo ci gaba sosai sannan suna ganin jam'iyyar APC a matsayin jam'iyyar da ta ke da maganin matsalolin jihar Abia.

Jiga-jigan PDP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi takwas a jihar Edo sun fice daga jam'iyyar PDP.

Jiga-jigan na PDP sun sauya sheƙs ne zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel