Tinubu Ya Kwashe Bayan Tsohon Shugaban PDP da Jiga-jiganta, Sun Watsar da Atiku

Tinubu Ya Kwashe Bayan Tsohon Shugaban PDP da Jiga-jiganta, Sun Watsar da Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake samun babban naƙasu bayan tsohon shugaban PDP ya watsar da kashinsa
  • Uche Secondus ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas a yau Alhamis
  • Daga cikin wadanda suka marawa Tinubu baya a taron akwai tsohon Ministan Sufuri, Abiye Sekibo da sauran jiga-jigan PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya nuna goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Secondus ya nuna goyon bayan ne da sauran mamabobin kwamitin kamfen ɗan takarar shugaban kasa a PDP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ana daf da buda baki, Buhari ya tura sako ga Tinubu, ya yi masa ruwan addu'o'i

Tsohon shugaban PDP ya watsar da Atiku, ya kama Tinubu
Tsohon shugaban PDP, Uche Secondus ya goyi bayan Shugaba Tinubu bayan marawa Atiku baya a zabe. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Uche Secondus.
Asali: Facebook

Tawagar PDP da suka marawa Tinubu baya

Tsohon shugaban PDP ya kuma marawa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers baya kan bayyukan alheri da ya ke yi, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, tsohon Ministan Sufuri kuma darakta-janar na kamfen PDP a Rivers, Dakta Abiye Sekibo shi ma ya bi sahun Secondus.

Tawagar jam'iyyar PDP ta bayyana haka ne a yau Alhamis 28 ga watan Maris a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers, cewar rahoton Vanguard.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Austin Okpara da tsohon gwamnan jihar, Tele Ikuru da Celestine Omehia.

Martanin Secondus kan matsalolin PDP

Secondus yayin da ya ke jawabi, ya ce Gwamna Fubara zai yi nasara a zaben da za a gudanar a 2027 duk da kalubalen da ya ke fuskanta.

"Zamu dawo da Fubara mulki a 2027, zai karbe ragamar wannan jam'iyyar a jihar Rivers gaba daya saboda shi ne shugaban jam'iyyar a jihar."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

- Uche Secondus

Tsohon shugaban PDP ya roki da a yafewa wadanda suka ci dunduniyar jami'yyar a zaben 2027, cewar theGuildNG.

Ya ba da tabbacin cewa jam'iyyar a matakin kasa ta na duk mai yiwuwa domin daukar mataki kan matsalolin.

'Yan Majalisa 6 sun koma jam'iyyar PDP

A baya, mun baku labarin cewa 'yan Majalisar jihar Enugu shida ne suka watsar da kashin jam'iyyar LP.

'Yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar saboda ayyakan ci gaba gwamnati mai ci ke samarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel