Matasan Najeriya
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa tsarin ilimin Najeriya ya bada gudumawar rashin aikin yi ga matasa. Dole ne a koyi sana'o'i.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke matashin da take zargin ya kashe tsohuwa mai shekaru 60. An kashe Safiya Yunusa ne a cikin gidanta da makami a Toro.
Gwamnatin tarayya ta tsawaita wa'adin masu sana'ar PoS na yin rijista da hukumar kula da kamfanoni, CAC, zuwa ranar 5 ga watan Satumbar 2024 domin 'yan karkara.
Shugaban hukumar NYSC ya yi nuni da cewa matasa masu yiwa kasa hidima za su amfana da sabon mafi karancin albashi. Ya nuna cewa za a yi musu karin alawus.
Daraktan hukumar NFC, Ali Nuhu ya ce za su ba matasa masu hidimar kasa ta NYSC gudumawar koyon sana'a. Ya fadi haka ne bayan ganawa da shugabar NYSC a Filato.
Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayar da gudummuwar N5bn domin karisa ginin sasanin NYSC, ya kuma yi alƙawarin ɗaukar likitoci daga cikin ƴan bautar kasa.
Gwamnatin jihar Kano ta ba kwamishinan shari'a umarnin dakile hanyoyin da masu safarar kwayoyi ke samun umarnin kotu na sakin kayansu da aka kwace.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da sanarwa kan fara biyan tallafin N150bn ga masu kananan sana'o'i da 'yan kasuwa a karshen watan Yunin 2024 da za mu shiga.
Wata babbar ma'aikaciyar gwamnati a jihar Abia ta shigar da wasu matasa su biyu kara babbar kotun jihar bisa zargin bata suna da suka mata. Ta nemi su biyata N100m
Matasan Najeriya
Samu kari