“Ba Na Bukatar Kowani Irin Namiji”: Budurwa Ta Bazama Neman Mijin Aure, Ta Fadi Irin Wanda Take So

“Ba Na Bukatar Kowani Irin Namiji”: Budurwa Ta Bazama Neman Mijin Aure, Ta Fadi Irin Wanda Take So

  • Wata kyakkyawar budurwa da ke ganiyar shekaru 30 da yan 'doriya ta sanar da neman mijin aure a dandalin X
  • Matashiyar na neman namiji wanda zai taimaka mata wajen gano ita din wacece sannan zai hadu da iyayenta bayan fara soyayyarsu da wata guda
  • Jama'a a dandalin X sun jinjinawa kwarin gwiwarta sannan suka yi mata addu'ar samun miji nagari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata jarumar mata yar Najeriya ta ayyana aniyarta na neman abokin rayuwa a dandalin X.

Matashiyar mai suna Adeshola Omo-eledumare (@tope_akan a manhajar X), wacce ke cikin shekaru 30 da 'doriya ta bayyana cewa tana bukatar namiji mai alkibla.

Matashiya na neman mijin aure
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: AzmanL/ Getty Images.
Asali: Getty Images

Budurwa na neman mijin aure

A cewar matashiyar wacce ke son nazari da rubuce-rubuce, ta ce tana ta zaman jiran namiji ya zo neman aurenta amma tunda hakan bai faru ba, ta yanke shawarar neman miji da kanta.

Kara karanta wannan

"Bana so na auri wacce bata san 'da namiji ba, akwai 'daga hankali": Jarumin fim ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa tana neman namijin da ba zai zo ya bata mata lokaci ko yi mata gwajin ta cancanci a aureta ba.

Adeshola ta jadaddawa jama'a cewa tana bukatar namiji wanda zai san darajarta.

Ta kara da cewar mijin da take so shine wanda zai mallaka mata abun da bai taba mallakawa wata diya mace ba, sannan zai je ya ga iyayenta wata guda bayan sun fara soyayya.

Ga wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Oma_G ta yi martani:

"Sai mutum mara tsoro da karfin gwiwa ne zai iya yin wannan. Ina maki fatan alkhairi Tope."

@Unli ta yi martani:

"Lallai za ki samu miji nagari da zai so ki kuma ya aure ki. Kin yi iya yinki ta hanyar fitowa sannan ki roki Allah."

@Royalgurly1 ta ce:

"Allah ya albarkace ki da namiji mai niyya da duk abin da zuciyarka ke so."

Kara karanta wannan

Kano: Yadda wani mutum ya aurawa malaminsa yaransa mata 2 a lokaci guda, an maka shi gaban Hisbah

@Royally inclnd ta ce:

"Yanzun nan na bi shafinki don ganin lokacin da za ki dawo ki ba mu labari mai dadi. Ina rokon Allah ya hada ki da namijin da ya dace, kema sai ki bi sa tare da zame masa mata tagari."

Matashi ya koka bayan samun karayar arziki

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya ba da labari mai ciwo na yadda rayuwarsa ta sauya ta tabarbare cikin dan kankanin lokaci.

Mutumin mai suna @king_cjohn a TikTok ya bayyana yadda kudadensa miliyoyin naira suka bi iska, lamarin da ya kai shi ga zama tamkar mabaraci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel