AFCON: Matashi Mai Bautar Kasa Ya Rasa Ransa a Jihar Arewa Kan Wasan Najeriya, Bayanai Sun Fito

AFCON: Matashi Mai Bautar Kasa Ya Rasa Ransa a Jihar Arewa Kan Wasan Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani matashi mai bautar kasa a jihar Adamawa yayin murna a gasar AFCON
  • Matashin da ke bautar kasa a Numan da ke jihar Adamawa mai suna Samuel ya rasa ransa ne yayin da ake buga fenaretin karshe
  • Kwadinetan hukumar NYSC a jihar, Mista Jingi Dennis ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Wani matashi da ke yi wa kasa hidima ya rasa ransa yayin kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.

Mai bautar kasar da aka bayyana da Samuel ya rasu yayin da ake buga fenareti bayan tashi a wasan, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Babban jigon APC ya yanke jiki ya mutu yayin da ya ke kallon wasan Najeriya

Mai bautar kasa ya mutu yayin kallon wasan Najeriya
Matashi Mai Bautar Kasa Ya Mutu a Jihar Adamawa Kan Wasan Najeriya. Hoto: Ahmadu Fintiri.
Asali: Twitter

Yaushe matashin ya mutu a Adamawa?

Rahotanni sun tabbatar cewa matashin da ke hidimar NYSC a Adamawa ya rasa ransa ne kafin buga fenaretin karshe da ya bai wa Super Eagles nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar ya ce Samuel ya mutu yayin murnar a wasan sami fainal a jiya.

Ya ce:

"Mun rasa dan Najeriya a jiya yayin murnar nasarar Super Eagles a gidan kallo da ke Numan.
"Matashin wanda ke yi wa kasa hidima a Numan ya fito daga jihar Kaduna ya suma kafin buga fenaretin karshe.
"Ya rasu kafin a kai shi asibitin Numan, Ubangiji ya masa rahama."

Martanin hukumar NYSC

Kwadinetan hukumar NYSC a jihar, Mista Jingi Dennis ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

Ya ce:

"Na samu labarin rasuwarsa jiya da dare muna tsammanin samun cikakken bayani a yau Alhamis.
"Abokinsa ya fada mana cewa sun je kallon kwallon tare amma ya fada musu ba ya jin dadin kallon fenareti a rayuwarsa.
"Ya sunkuyar da kansa inda daga bisani ya fadi, an tabbatar da mutuwarsa a asibiti da ke Numan."

Tsohon dan Majalisa ya mutu

Kun ji cewa jigon APC kuma tsohon dan Majalisar Tarayya a Najeriya ya riga gidan gaskiya.

Marigayi ya rasu ne yayin kallon wasan Najeriya da kasar Afirka ta Kudu a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel