Dan Yahoo Ya Caki Mahaifansa Saboda Sabulun Tsafi da Zai Kawo Masa Kudi Ya Ki Aiki, Laifinsu 1 Tak

Dan Yahoo Ya Caki Mahaifansa Saboda Sabulun Tsafi da Zai Kawo Masa Kudi Ya Ki Aiki, Laifinsu 1 Tak

  • Wani matashi mai suna Daniel Bamidele ya farmaki iyayensa biyu da sharbebiyar wuka, inda ya ji masu rauni
  • Matashin dai ya kasance yana harkar damfara ta yanar gizo don haka aka ba shi sabulun tsafi da zai dunga kawo masa kudi
  • Dole sai ya ambaci sunan mahaifiyarsa na gaskiya idan har yana son sabulun ya yi aiki, ya tambayeta sai ta fada mashi sunan karya, lamarin da ya fusata shi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani al'amari mai rikitarwa, wani matashi mai shekaru 20, Daniel Bamidele, ya soki iyayensa da sharbebiyar wuka a gidansu da ke garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Matashin wanda ke damfara ta yanar gizo (dan yahoo), ya aikata hakan ne saboda mahaifiyarsa ta ki fada masa sunanta na gaskiya wanda shine zai sa sabulun tsafi da aka ba shi don kawo masa kudi ya fara aiki.

Kara karanta wannan

An yi zanga-zanga yayin da malamin makaranta ya yi wa dalibi duka har sai da ya bakunci lahira

Matashi ya sari mahaifansa
Dan Yahoo Ya Sari Mahaifansa Saboda Sabulun Tsafi da Zai Kawo Masa Kudi Ya Ki Aiki, Laifinsu 1 Tak Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda mutanen gari suka ceto wasu ma'aurata a hannun dansu

Ba don agajin gaggawa da mutanen wajen suka kai ba, da Bamidele ya aika iyayensa lahira a ranar Alhamis, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa mahaifiyar matashin, Titilayo, ta fito daga gidansu da ke yankin Apabielesin a garin Ibadan da gudu dauke da munanan raunuka.

Ta fito ne tana ihun neman agaji yayin da dan nasu ya shiga cikin gidansu sannan ya farmake su da adda ita da mahaifinsa.

Ihun da ta yi ne ya janyo hankalin mutanen da ke tsaye, inda wasun su suka shiga gidan da gudu, suka danne yaron sannan suka karbe addan da ke hannunsa wanda da shi ya farmaki iyayen nasa.

Iyayena sun san ina damfara, Daniels

Yayin da makwabta suka karbe sharbebiyar wukar da ke hannunsa sannan suka kubutar da mahaifinsa, Daniel ya yi bayanin cewa yana samun abun hannunsa ne daga harkar damfara ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya gargadi Tinubu yayin da aka sace shugaban PDP, ya hango sabuwar matsala

Ya ce iyayensa na sane da cewar ya gina gidan kasa mai dakuna uku da abun da ya samu daga harkar damfarar ta yanar gizo.

Ya ce ya yi wa mahaifiyar tasa alkawarin bude mata babban shago da kaya don ta zama shahararriyar yar kasuwa da zaran hakarsa ta cimma ruwa.

Ya kara da cewa mahaifiyarsa da yayensa suka hada baki suka raba shi da kudi har naira miliyan 2.5, duk da alkawarin da ya yi na bude mata shago da kayayyaki, rahoton LIB.

Daniel ya ce:

"Da gangan na yi wa mahaifiyata dabara daga wajen wani taron cocin da take zuwa, kuma da isarmu gida, na farmaketa da wuka sannan na fara yanyankata lokacin da mahaifina ya yi kokarin ceton ta.
"Na farmaki mahaifina ne shima saboda idan ban caki su biyun ba, za su yi nasara wajen kashe ni."

Mahaifiyata ta lalata sabulun da aka bani, Matashi

Kara karanta wannan

"Matata ta mayar da hankali kan harkokin addini bata kula da ni", miji ya nemi a raba aurensu

Da yake ci gaba da bayyana dalilinsa na farmakar iyayensa da wuka, Daniel ya zargin mahaifiyarsa da fada masa sunan karya wanda ya bata sabulun tsafi da aka ba shi a wani coci.

Ya kuma bayyana cewa yayansa ya saka a matsayin wanda zai gaje shi a banki amma kuma shi din yana ta kokarin yi masa wasa da kudadensa.

Ya ce:
"Ina fushi da iyayena, musamman mahaifiyata, saboda ta bani sunan karya maimakon sunanta na gaskiya.
"Akwai wani sabulun tsafi da aka bani da nake amfani da shi a baya-bayan nan. Wani limamin coci mai suna Mathew ne ya bani.
"An hada sabulun ne don ya kawo mani alkhairi, amma akwai bukatar na ambaci sunan mahaifiyata kafin ya yi aiki.
"Mahaifiyata ta fada mani cewa sunanta Titilayo, amma da na ambaci sunan a sabulun, bai yi aiki ba. Saboda haka, na fusata sannan na yake shawarar tsere ta."

Karya yake ban karbi kudinsa ba, Titilayo

Kara karanta wannan

Jibrin dan Sudan: Mai daukan Buhari hoto ya magantu kan zargin sauya tsohon shugaban kasar

Sai dai kuma, mahaifiyar matashin ta karyata cewar ta karbi kudi daga hannusa.

"An kira ni a waya cewa na zo na dauki dana daga makarantar LAUTECH lokacin da ya fara nuna lalura ta tabin hankali.
"Da muka dawo gida, sai mahaifinsa ya kawo maganin gargajiya sannan ya ba shi ya yi amfani da shi. Bacci ya kwashe shi bayan ya sha maganin.
"Amma kuma, da ya tashi sai ya bukaci ina wayarsa sai na fada masa ban dauki wayarsa ba. Ya yi mun nauyi da dama.
"Makaryaci ne shi, ban karbi kowani kudi daga hannunsa ba.

Mahaifin matashin ya magantu

Sai dai kuma mahaifin Bamidele ya zargi matarsa da masaniya a kan yadda aka yi dansa ya fara damfara ta yanar gizo da kuma yadda ya gina wani gida daga kudin da ya samu a hankar.

“Matata ce ta ba shi (Daniel) goyon baya. Ta san lokacin da danta ya fara gina gida, amma ba ta gaya mani ba,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel