Manoma na cikin Alheri, Gwamnati Za Ta Raba wa Ƴan Najeriya Dala Miliyan 500
- Shugaban hukumar hada-hadar kudin hadin gwiwa ta kasa, Emmanuel Atama, ya bayyana shirin ba manoma bashin makudan kuɗi
- Ya tabbatar da cewa bashin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya zai kai ga manoma na gaskiya
- Emmanuel ya ce matsalolin baya sun hada da rashin bayani da tsoma bakin siyasa, amma yanzu an gyara tsarin domin tabbatar da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban hukumar hada-hadar kudin hadin gwiwa ta kasa, Emmanuel Atama ya yi wa manoma albishir na samun rancen kudi.
Atama ya tabbatar da cewa bashin dala miliyan 500 zai kai ga manoma na gaskiya a Najeriya cikin sauki.

Source: Facebook
Tsarin da aka dauko na rabawa manoma tallafi
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Trust TV, inda ya ce shirye-shiryen baya sun gaza isa ga manoma saboda rashin isasshen bayani da kuma tsoma bakin siyasa.
Atama ya ce wannan karon zai bambanta saboda akwai minista mai kishin hadin gwiwa, wanda ke cire duk wata matsala da ke hana aiwatar da shirin yadda ya dace.
Ya kara da cewa a baya ba a gayyaci hukumar tasu domin bayar da gudunmawa ba, amma yanzu an ba su damar taka rawa a cikin shirin.
Ya ce Bankin Duniya ya bayyana wasu kurakurai da suka faru a shirin Anchor Borrowers, inda ya ce ba za su bari a sake yin irin wadannan kuskure ba.

Source: Facebook
Yadda ake wayar wa manoma kai kan shirin
Atama ya kara da cewa tun bayan sanar da shirin, sun fara wayar da kan manoma a yankuna daban-daban domin shiga cikin tsarin ta hanyar kungiyoyin hadin gwiwa.
Ya bayyana cewa za a bayar da bashin ne galibi ta hanyar kayan noma domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudin yadda ya kamata.
Ya ce idan har za a ba manoma kudi, to zai kasance kadan ne, kimanin kashi 10 zuwa 15 cikin dari kacal.
Ya kara da cewa matsalar da ake fuskanta a baya ita ce manoma suna rarrabe, wanda ke ba wasu damar guduwa da kudin bashin.
Amma yanzu, ya ce suna shirin amfani da tsarin noma na rukuni, inda za a hada manoma a wuri guda domin saukaka gudanar da ayyuka.
Ya bayyana cewa duk lokacin da za a fara aikin gyaran gona, za a sanar da duk manoman, sannan a yi aikin ta hanyar tsari na tsakiya.
A karshe, ya ce kudin aikin za a cire shi kai tsaye daga asusun kowane manomi domin biyan kudin da aka kashe cikin gaskiya da tsari.
Manoma 3,500 za su hakura da noma
A baya, an ji cewa manoman shinkafa dubu uku da dari biyar na shirin barin aikin noma bayan tafka asarar Naira biliyan 93 sakamakon shigo da shinkafar waje.
Rahoton fadar shugaban kasa ya nuna cewa manoma da dama sun koma noman ridi da waken soya wadanda suka fi riba a kasuwar duniya.
Masana sun ba wa gwamnatin tarayya shawararwarin yadda za a kare manoman kasar daga asara da kuma kare kasar daga karancin abinci.
Asali: Legit.ng

