Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Halaka Shugabannin Matasa 2 a Jihar PDP

Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Halaka Shugabannin Matasa 2 a Jihar PDP

  • Wasu mutane ɗauke da bindigu sun halaka shugabannin matasa biyu kisan gilla a jihar Delta ranar Litinin
  • Tsohon sanata a jihar, Chief Ighoyota Amori, ya yi tir da wannan kisan, inda ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran al'umma
  • Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su tashi tsaye kana su tabbata sun kamo makasan domin doka ta yi aiki a kansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugabannin matasa biyu a Mosogar da ke karamar hukumar Ethiope ta Yamma a jihar Delta a ranar Litinin da ta wuce.

Waɗanda aka kashe sun haɗa da, Mista Godwin Ogberahwe, shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar matasan Mosogar da kuma Mista Efe Oki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kisan da aka yi wa sarakunan gargajiya, ya bayar da sabon umarni

IGP Kayode.
Yan Bindiga Sun Halaka Shugabannin Matasa 2 a Jihar Delta, Sanata Ya Yi Allah Wadai Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, wasu mahara da har yanzun ba a tantance su waye ba, su ne suka halaka matasan biyu cikin sa'o'i ƙalilan ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya yi magana kan wannan kisan

Tsohon sanatan jihar Delta, Chief Ighoyota Amori, ya yi tir da wannan ɗanyen aiki inda ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalai, ƙunguyar matasa da ɗaukacin mazauna Mosogar.

Ya kuma bayyana cewa labarin kisan jagororin matasan guda biyu ya gigita shi matuƙa, yana mai cewa abin takaici ne irin haka ta riƙa faruwa a tsakanin matasa.

A cewarsa, abin bakin ciki ne yadda matasa za su dauki bindigu su fara farauta ko kashe ’yan uwansu matasa ba tare da jin wani abu ko nadama ba a cikin al’umma.

"Dole jami'an tsaro su kamo makasan"

Da yake Allah wadai da lamarin, ya bayyana cewa ya zama tilas a dawo da waɗannan yara kan hanya. Ya ce:

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fashe da kuka ana cikin zaman majalisa, an fadi dalili

"Abin takaici, jimami da tir ne wannan kisan gilla na rashin hankali da aka yi wa waɗannan matasa biyu, 'ya'ya a yankin Mosogar.
"Ina kira ga hukumomin tsaro su tashi tsaye kana su zage dantse wajen sauke nauyin aikinsu na tsare rayuka da dukiyoyin al'umma domin kare faruwar haka a gaba.
"Ya zama wajibi a yi bincike mai zurfi kana a kwamuso waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki domin su gurbi abinda suka shuka a gaban ƙuliya."

Ƴan bindiga sun kashe yan sanda a Imo

A wani rahoton kuma Yan sanda da wasu mutane sun rasa rayuwansu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari mai muni a titin Owerri zuwa Orlu a jihar Imo.

Wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun kashe ƴan sanda biyu da ke bakin aiki tare da wasu mutum 2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262