Matashi da Ya Mallaki Naira Miliyan 30 Ya Samu Karayar Arziki, Ya Koma Rokon N2k

Matashi da Ya Mallaki Naira Miliyan 30 Ya Samu Karayar Arziki, Ya Koma Rokon N2k

  • Wani matashi dan Najeriya ya koka da hawaye yayin da ya tuna yadda karayar arziki ta same shi da halin da yake ciki a yanzu
  • A wani bidiyo da ya yadu, ya bayyana cewa a baya yana da kudi naira miliyan 30 a asusunsa amma kuma yanzu ya koma rokon taro kwabo
  • Susan Nweke, wata tsohuwar ma'aikaciyar banki, ta ba jaridar Legit labari makamancin wannan na yadda dukiyarta suka kone kurmus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya ya ba da labari mai ciwo na yadda rayuwarsa ta sauya ta tabarbare cikin dan kankanin lokaci.

Mutumin mai suna @king_cjohn a TikTok ya bayyana yadda kudadensa miliyoyin naira suka bi iska, lamarin da ya kai shi ga zama tamkar mabaraci.

Kara karanta wannan

Ana daf da auren malamin makarantar allo, matsafa sun yanke mazakutarsa a Zaria

Matashi ya samu karayar arziki
Matashi da Ya Mallaki Miliyan 30 Ya Samu Karayar Arziki, Ya Koma Rokon N2k Hoto: @king_cjohn/TikTok
Asali: TikTok

Matashi ya zub da hawaye saboda karayar arziki

Abun bakin ciki, yanzu ya zama talakan talak yayin da ya koma rokon N2k daga wajen mutane don ya samu na sanyawa a bakin salati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bayar da labarinsa cikin hawaye, mutumin ya roki Allah da ya dawo masa da arzikinsa sannan ya sake daukaka shi.

Ya rubuta:

"Mutumin da ya ga naira miliyan 30. Yanzu yana rokon 2k. Ka dawo da ranakun samu ya ubangiji."

Da take zantawa da jaridar Legit, wata yar Najeriya, Susan Nweke, ta tuna yadda rayuwa ta juya mata baya bayan an sallame ta daga wajen aiki.

"An sallame ni daga wajen aikina sannan rayuwata ta zama mara amfani. Ban yi tsammanin hakan ba lokacin da ya faru. Yanzu Allah yana taimakona, inji ta.

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Abba Gida-Gida ya sauko daga motarsa don ba wata hakuri, sun bugi motarta ne

@chickweedyoung.Deroy ya ce:

"Idan na ga abun da ya kai naira miliyan 30 ba zan sake talauci ba, ba zan sake ba koda kuwa kudin daga hannun tsafi ya fito."

Domsmugo42 ya yi martani:

"Duk wanda hakan bai taba samunsa ba zai yi tunanin cewa mutanen da suka yi arziki suka samu karayar arziki basu yi amfani da kudinsu yadda ya dace bane."

Q FrOsH ya yi martani:

"Ka je lekki ko baka je ba."

@paygevibes ya ce:

"Wanda ya nemi kudi bai zuba jari ba zai sake nemansu."

Budurwa ta rabu da sahibinta saboda karayar arziki

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashi wanda bai ji da daɗi ba a hannun wata budurwa wacce ya taimaka a baya, ya dawo domin ɗaukar fansa.

Matashin shi ne ya taimaka mata ta buɗe shagon siyar da kayan sawa, amma daga baya sai budurwar ta rabu da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel