An Kawo Sababbin Dokokin BVN da za Su Shafi Aiki da Banki a Najeriya
- CBN ta gabatar da sababbin dokokin BVN da za su fara aiki daga 1 ga Mayu, 2026, domin dakile zamba da kuma inganta kare bayanan jama'a
- Masu asusun banki za su iya sauya lambar wayar da aka hada da BVN sau daya kacal a rayuwarsu domin hana damfarar mutane a kasar nan
- Sababbin dokokin sun hada da iyakance mu’amaloli da kuma amfani da manhajar banki guda daya kacal domin kara tsaron asusun bankuna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) na shirin fara amfani da sababbin dokokin BVN daga ranar 1 ga Mayu, 2026, a wani mataki na dakile zamba, karfafa kariyar bayanan mutane da kuma kare tsarin hada-hadar kudi na kasar.
Sabon tsarin ya kawo tsauraran ka’idoji kan sauya lambar waya, amfani da na’urori da kuma iyakance mu’amaloli, wanda ke nuna babban sauyi a yadda ‘yan Najeriya ke amfani da asusun bankinsu da kuma kare su.

Source: Facebook
Tribune ta rahoto cewa CBN ya bayyana manyan sauye-sauye guda 10 a dokokin BVN da za su fara aiki daga ranar 1 ga Mayun 2026.
Dakokin BVN 10 a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa sababbin dokokin za su shafi yadda kwastomomi ke shiga manhajojin banki, canza na’ura da kuma sarrafa bayanan BVN dinsu.
TVC ta wallafa cewa manyan sauye-sauyen sun hada da:
1. Manhajojin banki za su takaita ga amfani da na’ura (waya) daya a lokaci guda.
2. Da zarar mutum ya fara amfani da wata na'ura (Waya) za a cire bayanan manhajar bankinsa a tsohuwar da ya bari
3. Canza na’ura zai jawo bukatar a tantance mutum
4. Za a sanya ido a kan BVN da ake zargi
5. Bankuna na iya takaita ko daskarar da asusun da ke da alaka da BVN da aka yi wa alamar zargi
6. Abokan hulda za su iya sauya lambar wayar BVN sau daya kacal daga ranar da dokar ta fara aiki
7. Doka za ta dakile damfara ta hanyar sauya layin waya
8. Mutane masu shekaru 18 zuwa sama ne kawai za su iya yin BVN daga 1 ga Mayu, 2026
9. Yara 'yan kasa da shekara 18 za su yi amfani da banki karkashin kulawar iyaye ko wakilansu
10. Za a iyakance tura kudi daga sabuwar na’ura (Manhaja) zuwa Naira 20,000 a cikin sa'o'i 24 da bude ta, wanda a yanzu ya kai N50,000.

Source: Facebook
Dalili saka dokar BVN a Najeriya
Babban bankin ya ce wadannan matakai na cikin wani babban shiri na kara tsaron tsarin banki a Najeriya da rage zamba da ke da alaka da mu’amalolin zamani.
Da yake sababbin dokokin za su fara aiki nan ba da jimawa ba, ana shawartar kwastomomi su dauki matakai domin kauce wa matsaloli.
CBN bai fito da sabon kudi ba
A wani labarin, mun kawo muku cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata cewa ya kawo sabuwar takardar kudi a kasar nan.
Bankin ya yi karin haske ne bayan jama'a da dama sun yada cewa an kawo sabuwar takardar N5,000 a Najeriya a kafafen sada zumunta.
A hoton sabuwar takardar kudin bogin da aka wallafa, an sanya hoton shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


