“An Hada Miliyan 17”: Yan Najeriya Sun Hadawa Wani Dattijo da ke Aikin Kera Bulo Kudade

“An Hada Miliyan 17”: Yan Najeriya Sun Hadawa Wani Dattijo da ke Aikin Kera Bulo Kudade

  • Yan Najeriya sun tarawa wani dattijo da aka gano yana aiki tukuru a karkashin rana kudade masu yawan gaske
  • Wani rubutu da aka wallafa a dandalin X ya nuna cewa an tarawa mutumin da ke aikin kera bulo duk da tsufansa naira miliyan 17
  • An gano mutumin yana aiki a duke, wanda hakan ke nuna watakila yana fama da ciwon baya amma duk da haka yake aiki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya da matarsa sun taki sa'a yayin da bayin Allah suka yi masu sha tara ta arziki ta hanyar tattara masu kudade.

Wata wallafa da Ajewole Esq ya yi a soshiyal midiya ya nuna cewa an tarawa mutumin da matarsa kudi fiye da naira miliyan 17.

Kara karanta wannan

"Ya hadu sosai": Matar aure ta cika da farin ciki yayin da mijinta ya wanke mata kayanta a bidiyo

Yan Najeriya sun gwangwaje tsoho mai aikin gina bulo
“An Hada Miliyan 17”: Yan Najeriya Sun Hadawa Wani Dattijo da ke Aikin Kera Bulo Kudade Hoto: X/@0oni0fife.
Asali: Twitter

Lamarin ya fara ne a lokacin da wani bidiyo ya hasko mutumin yana aiki cikin rana mai zafi duk da tsufansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da suka ga bidiyon sun tausaya masa saboda ganinsa yana lailaya bulo yayin da yake tsaye a duke.

Daga ganin yanayin yadda yake tafiya da dukewarsa, mutane suka yi tunanin cewa wata kila yana da lalurar ciwon baya.

An tarawa mai aikin kera bulo naira miliyan 17

Karin bayanin da Ajewole ya yi ya nuna cewa an dauki mijin da matar tasa zuwa asibiti don duba.

Ajewole ya ce:

"An tara miliyan 17 da yan 'doriya. Shi da sahibarsa suna samun kulawar likitoci. Muna godiya kan komai. Allah ya albarkaci duk hannayen da suka sa hakan ya zama gaskiya."

Kalli hotunan a kasa:

Jama'a sun yi martani

@LifeOfNapaul ya ce:

Kara karanta wannan

Matashi da ya mallaki naira miliyan 30 ya samu karayar arziki, ya koma rokon N2k

"Ina da tabbaci dari bisa dari cewa yana amfani da maganin ciwon baya ne wajen yin wannan."

@Abigailsam18 ta yi martani:

"Irin wadannan mutanen ne ya kamata mu dunga yi wa sha tara ta arziki lokaci zuwa lokaci."

@Kendy__x ya yi martani:

"Matarsa na da kyau sosai, Allah ya albarkace ki."

@Ayoflagos8 ya ce:

"Ka auri mace ta gari, faaaa.Akwai dalili. Ka yi tunanin abun da su biyun suka fuskanta kuma matar bata rabu da shi ba."

Miji ya ririta matarsa a bidiyo

A wani labarin kuma, wata matar aure ta yada bidiyonta cikin farin ciki bayan ganin mijinta yana hada kayanta domin ya tayata wanke su.

A cikin bidiyon na TikTok, an gano mutumin dauke da murmushi yayin da matar tasa ta fara yi masa kirari kan abun da yake shirin yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel