“Kada Ku Mayar da Kudi Ubangijinku”: Tinubu Ya Ba Shugabannin Kirista Babban Aiki 1 Tak

“Kada Ku Mayar da Kudi Ubangijinku”: Tinubu Ya Ba Shugabannin Kirista Babban Aiki 1 Tak

  • Shugaban kasa Tinubu ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya bayan ya gana da shugabannin kungiyar CAN
  • Tinubu ya bayyana cewa yan Najeriya za su iya bayar da gudunmawarsu don ci gaba da bunkasa kasar tare da sauya tunaninsu kan kudi
  • Sai dai kuma, ya bukaci shugabannin kungiyar Kiristocin da su yi wa'azin da ya dace wanda ya karkata kan fahimta, hakuri da juriya, da fata ga yan Najeriya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen magance cin hanci da rashawa da sauran munanan dabi'u.

Kara karanta wannan

"An yi masa mugun duka": Shehu Sani ya yi martani yayin da shugaban makarantar Kaduna ya shaki yanci

A cewarsa, aikin tsarkakewa ne tabbatar da ganin cewa an saita kasar zuwa tafarki madaidaiciya don ci gaban dukkanin yan Najeriya.

Tinubu ya bukaci shugabannin Kirista su mara masa baya
“Kada Ku Mayar da Kudi Ubangijinku”: Tinubu Ya Ba Shugabannin Kiristoci Babban Aiki 1 Tak Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Ya bukaci yan Najeriya da su hada hannu wajen gyara kasar sannan su sauya tunaninsu a kan kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya nemi goyon bayan kungiyar CAN don yakar rashawa a Najeriya

Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) karkashin jagorancin shugabanta Archbishop Daniel Okoh a adar shugaban kasa Abuja, rahoton Channels TV.

Shugaban Najeriyan ya bukaci kungiyar Kiristocin da ta taimaka wajen yin wa'azi kan cin hanci da rashawa da batutuwa masu alaka, rahoton TVC News.

A cewar sanarwar dauke da sa hannun kakinsa, Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce:

"Ba mu da wata kasar sai Najeriya. Idan ba ku yi wa'azin fahimta, hakuri da juriya da fata ga yan Najeriya ba, kuna illata kasar ne, kuma babu wanda zai taimaka mana wajen gyara ta."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da tawagar ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN a Villa, bayanai sun fito

Sai dai kuma Tinubu ya ba da tabbacin taiya da kowa a gwamnatinsa, yana mai alkawarin yin adalci ga dukkan yan Najeriya.

Jigon PDP ya magantu akan maja

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon dan takarar gwamna a jihar Ogun kuma jigon jam'iyyar PDP, Hon. Segun Showunmi, ya bayyana dalilan da suka jam'iyyar hadin gwiwa ba za ta yi tasiri a kan APC ba a 2027.

A wata hira da jaridar Punch ta wallafa a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, jigon na PDP ya bayyana cewa dabarar da APC ta yi amfani da shi wajen tsige PDP a 2015 ba lallai ne ya yi aiki ga yan adawa a 2027 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel