Albashin ma'aikatan najeriya
Daga N30, 000, mafi karancin albashi zai iya dawo N1000000. Idan ba a shawo kan hauhawar farashi ba, NLC za ta kawo dogon buri wajen maganar karin albashi.
Ma’aikatan gwamnatin tarayya a ma’aikatu da hukumomi kusan 90 har yanzu ba su samu albashin watan Janairu ba. Ma'aikatan dai tuni suka fara yin korafi akan jinkirin.
Osita Okechukwu ya ce akwai hadari idan aka tashi mafi karancin albashi sosai, ya ce gwamnati tayi hattara, kul ta biyewa NLC wajen laftawa ma’aikata kudi.
Godwin Abumusi, shugaban kungiyar 'yan fansho na Najeriya ya ce za su fita titi su yi zanga-zanga zindir idan har gwamnati ba ta kara fansho mafi karanci ba.
An ji cewa Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa za a biya ma’aikata N10, 000 a rage radadin tsadar fetur. NLC ta ce wannan ya yi kadan a halin da ake ciki.
Ma’aikatan gine-gine sun tafi yajin-aikin kwana 3 daga yau. Kungiyoyi sun ce rayuwa tayi wahala amma an bar su cikin kunci tuni wasu gwamnatoci sun yi karin albashi.
Ma'aikatan tarayya sun fara 'yan guna-guni yayin da gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na yin albashi a ranar Alhamis, kuma ba a biya su naira dubu 35 ba.
An bar maganar N30, 000, NLC ta ce ya kamata mafi karancin albashi ya zama $300 ne a wata. 'Yan kwadago ba su yanke wani albashi ba, amma N200, 000 ya yi kadan.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na’am da kafa kwamiti na musamman da zai duba lamarin yin karin albashi, mun kawo cikakken jerin ‘yan kwamiti.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari