Bayanai Sun Fito Yayin da Likitoci Fiye da 50 Suka Ajiye Aiki Suka Bar Marasa Lafiya

Bayanai Sun Fito Yayin da Likitoci Fiye da 50 Suka Ajiye Aiki Suka Bar Marasa Lafiya

  • Akalla likitoci 59 ne suka ajiye aiki a asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH) dake Lafiya, jihar Nasarawa saboda rashin albashi mai tsoka
  • Ajiye aikin likitocin ya biyo bayan yajin aiki da zanga-zangar da likitoci suka rika yi domin gwamnati ta biya bukatunsu amma abin ya ci tura
  • Ya zuwa yanzu dai an fara ganin tasirin ajiye aikin likitocin a DASH yayin da marasa lafiya ke jira na tsawon sa'o'i kafin su samu ganin likita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasarawa - Likitoci 59 da ke aiki da asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH) dake Lafiya sun ajiye aikinsu a gwamnatin jihar Nasarawa.

Sun ajiye aikin ne saboda rashin samun albashi mai tsoka da alawus-alawus, da kuma rashin samun kyakkyawan yanayi na gudanar da aiki a cikin watanni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Likitoci a jihar Nasarawa
Rashin alawus da karin girma ya tilasta likitoci ajiye aiki a Nasarawa. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa likitoci 20 sun tafi Saudiyya yayin da 39 suka yi murabus saboda rashin albashi mai tsoka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin shekaru biyu da suka gabata, manyan asibitoci mallakin gwamnatin jihar Nasarawa sun rasa ma'aikata da dama.

Mutane 25 sun yi murabus a kwana 2

Hakan ya biyo bayan yawan yajin aiki da zanga-zangar da ma'aikatan kiwon lafiya musamman likitoci suka yi saboda rashin samu albashi da alawus alawus.

Radio Nigeria ta ruwaito cewa lamarin ya kara ta’azzara bayan ajiye aikin da likitoci sama da 50 suka yi a jihar a tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2024.

Wani babban jami’in gwamnati a sashin gudanarwa na DASH ya shaida wa jaridar cewa, a cikin kwanaki biyu sun samu wasikun ajiye aiki daga likitoci sama da 25.

Kara karanta wannan

N11,000/50kg: Hauhawar farashin siminti da matsalolin da yake haifarwa a Najeriya

Likitoci a Nasarawa na kuka da gwamnati

Shugaban kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Nasarawa, Dakta Yakubu Adeleke, ya bayyana cewa tun a shekarar 2022 suke tuntubar gwamnatin jihar domin ta gaggauta magance bukatunsu amma kokarin yi ya ci tura.

Dr. Adeleke ya ce murabus din da likitocin suka yi a baya-bayan nan zai kara matsin lamba kan tsarin kiwon lafiya a jihar.

Wasu daga cikin likitocin da suka zanta da manema labarai a jihar, sun ce hakurin su ne ya kare.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi martani

Sai dai kwamishinan lafiya na jihar, Dr Gaza Gwamna, ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta fara aiwatar da biyan kudaden alawus ga likitoci a jihar.

Ya yi kira ga sauran likitoci da su kwantar da hankalinsu, inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta fara aikin daukar ma’aikata domin cike guraben likitocin da suka ajiye aiki.

Kara karanta wannan

Tsohon sarkin Kano, Sanusi ya fashe da kuka a wajen makokin Herbert Wigwe, bidiyo

Ya zuwa yanzu dai an fara ganin tasirin ajiye aikin likitocin a DASH yayin marasa lafiya ke jira na tsawon sa'o'i kafin su sami damar ganin likita.

Jihohi masu yawan kwararrun likitoci

A wani labarin, Legit Hausa ta yi nazari kan yadda Najeriya ta gaza cika muradin hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) na samar da wadatattaun likitoci da za su kula da marasa lafiya.

A shekarar 2023, ministan kwadago na wancan lokaci, Chris Ngege ya nuna fargaba kan yadda kasar ba za ta iya samar da likita daya kan marasa lafiya 600 ba.

A wannan labarin, Legit ta tattaro bayani kan jerin jihohin Najeriya da suka fi yawan kwararrun likitoci, da yawan mutanen da suke iya dubawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel